Na Fuskanci Barazanar Kisa Akan Aikina – Pantami

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami yayi bayanin kalubalen da ya fuskanta saboda ya kawo tsarin NIN wato tsarin haɗa layin waya da shaidar zama ɗan ƙasa. A ranar Juma’a 16 ga watan Satumba 2022 Jaridar Daily Trust ta yi rahoto Isa Ali Ibrahim Pantami yana cewa ya fuskanci barazanar kisa a kujerar Minista. Pantami yace yunkurin yi wa kowane layin waya rajista da lambar NIN ta jawo masa wannan barazana. Ministan ya bayyana haka…

Cigaba Da Karantawa

An Bankado Kazamar Cuwa-Cuwa A Shirin Ciyar Da Dalibai

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a wani sabon magudi da aka bankado a aikin ma’aikatar jinkai da jin dadin al’umma, gwamnatin tarayya ta bankado makarantun karya 349 a jihar Nasarawa. Kwamitin tattara bayanai na shirin ciyar da daliban makarantu na gwamnatin tarayya ce ta bankado wannan almundahanan. Mallam Abdullahi Usman, wanda shine shugaban kwamitin kuma mai baiwa ministar jinkai Hajiya Sadiya Umar shawara ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai wajen gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule. A cewarsa, wasu jami’an ma’aikatar ke cinye…

Cigaba Da Karantawa

Kano: An Damke Dan Chanan Da Ya Yi Wa Budurwa Yankan Rago

Shaidun gani da ido sun tabbatar da faruwar lamarin wanda bayanai ke cewa ya faru ne da misalin karfe 9 na daren ranar juma’a kamar yadda wani makwabcin gidan da abin ya faru Abubakar Mustpha ke cewa yarinyar da aka bayyana sunanta da Ummita wadda daliba ce a kwalejin horar da Ungozoma da malaman jinya ta jihar Kano, bazawara ce kuma ana ganinsu lokaci zuwa lokaci da dan Chinan.   A cewar wasu bayanai yarinyar wadda cikakken sunanta shi ne Ummakulsum Sani Buhari mazauniyar unguwar Janbulo da ke karamar hukumar…

Cigaba Da Karantawa

Gayyatar Yariman Saudiyya Jana’izar Sarauniya Ya Haifar Da Surutai

Gayyatar da Birtaniya ta yi wa Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman zuwa jana’izar Sarauniya ya janyo zanga-zanga daga masu rajin kare hakkin bil-adama. Wani rahoto da hukumar leken asirin Amurka CIA ta fitar ya nuna cewa Yariman na Saudiyya na da hannu wajen kisa tare da daddatsa gawar dan jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya. Sai dai a lokuta da dama Yariman na Saudiyya Muhammad Bin Salman ya musanta wannan zargi da ake yi masa tare da…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Zai Ziyarci Amurka Yau Lahadi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi taro kasar Amurka yau Lahadi. Buhari zai halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara karo na 77 da za a gudanar a birnin New York na ƙasar ta Amurka. A wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya fitar a shafinsa na Tuwita, ya ce shugaban zai gabatar da jawabi a ranar Laraba a taron da shugabannin kasashen duniya za su halarta.

Cigaba Da Karantawa