Gwamnatin Borno, Bizi Mobile, Kama Integrated Da BRMFB Sun Horar Da Matasa Shirin e-Naira

Daga Wakilinmu A kokarinsu na ganin sun samarwa da Matasa ayyukan yi, Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Zulum, da hadin gwiwar kamfanin hada hadar kudi irin na zama ni, wato Bizi Mobile Cashless Consultant limited, da kamfanin Kama Integrated Services limited da kuma BRMFB, sun horar da Matasan Jihar Borno Maza da Mata har su kimanin 270 harkar Agency Banking da kuma basu horo na musamman akan shirin Babban bankin kasa (CBN) akan harkar e-Naira. Taron horarwar na musamman wanda aka shirya shi na yini biyu, ya gudana…

Cigaba Da Karantawa

‘Yar Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ta Roki ‘Yan Najeriya Koda

Sonia, diyar sanata Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, ta roki jama’a da su taimaka mata da gudunmawar koda. Diyar dan majalisar ta yi wannan rokon ne a daidai lokacin da iyayenta suka shiga tsaka mai wuya a kokarinsu na ceto rayuwarta. An kama Ekweremadu da matarsa a watan Yuni lokacin da suke kokarin samawa Sonia gudunmawar koda daga wani matashi a birnin Landan, an gurfanar da ma’auratan a gaban kotu kan zargin safarar mutum da kokarin cire wani sassa na jikin karamin yaro da bai balaga ba. Daga…

Cigaba Da Karantawa

Taraba: Tsohon Gwamna Jolly Nyame Ya Samu Kyakkyawar Tarba

Labarin dake shigo mana daga jihar Taraba na bayyana cewar Jolly Nyame, tsohon gwamnan jihar a cikin ranakun karshen mako ya samu kyakkyawar tarbar girma daga jama’a bayan ya dawo Taraba sakamakon rangwamen da ya samu. A watan Afirilu, taron majalisar zartarwa ta kasa wacce ta samu jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta yi rangwame ga mazauna gidan yari 159 da suka hada da Nyame da Joshua Dariye tsohon gwamnan Filato. Tsoffin gwamnonin wadanda aka garkame sakamakon cin amanar kasa da damfara, an yi musu rangwame saboda shekarunsu da kuma halin…

Cigaba Da Karantawa

Ana Satar Danyen Mai Na Dala Miliyan 700 Duk Wata A Najeriya – NNPC

Babban Manajan Kamfanin NPMS, reshe daga kamfanin fetur na ƙasa, NNPCL, Bala Wunti, ya ce a duk wata ana satar ɗanyen mai aƙalla ganga 470,000 a ƙasar nan. Wunti ya yi wannan bayani lokacin da ya ke rangadin duba kadarorin NNPCL. Ya ce an ƙiyasta ɗanyen man da ake dacewa ɗin duk wata zai kai na dala miliyan 700. Sannan ya ce rabon da bututun mai na Bonny Terminal ya yi aiki tun cikin watan Maris, saboda ɓarayin ɗanyen mai masu fasa bututu. Ya ce wannan matsala ta haifar wa…

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aiki: Kotu Ta Dage Saurarar Karar Da Gwamnatin Tarayya Ta Kai ASUU

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotun masana’antu a ranar Litinin ta dage sauraron sharia’a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i, ASUU, zuwa ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa. Mai shari’a Polycarp Hamman ya dage sauraron shari’ar ne saboda a bai wa gwamnatin tarayya mika dukkan takardun da suka dace don karar, wadda ke ƙalubalantar matakin da kungiyar malaman ta ɗauka na kassara ilimi a ƙasar. Channels TV ta rahoto. KARA KARANTA WANNAN Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU…

Cigaba Da Karantawa