An Sake Bankado Zunubban Abba Kyari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta bankaɗo wasu kadarori 14 mallakar tsohon shugaban rundunar tattara bayanan sirri ta hukumar ‘yan sandan kasar DCP Abba Kyari. An ruwaito cewa kadarorin sun hadar da manyan kantunan sayayya, da gidaje, da filin wasan polo, da filaye tare kuma da gonaki. An zargi Kyari da kin bayyana kadarorin nasa dake wurare daban-daban a birnin Tarayya, Abuja da birnin Maiduguri na jihar Borno. An kuma gano sama da naira miliyan 207 da euro 17,598 a asusun ajiyarsa…

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aikin ASUU Na Iya Haifar Da Babbar Fitina A Najeriya – Masana

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar tsofaffin daliban jami’i’on gwamnatin tarayya, ta yi gargadin cewa yajin aikin da kungiyar malaman jami’a ta ASUU ke yi ka iya zama babban bala’i ga kasar. A wata wasika da kungiyar ta fitar a ranar Litinin, ta yi kira ga gwamnati da ASUU su sake zama teburin sulhu domin magance matsalar. Sama da watanni shida kenan da ASUU ta tsunduma yajin aiki a daukacin Najeriya, ko da yake wasu gwamnatocin jihohin Najeriya sun kira malamai su koma bakin…

Cigaba Da Karantawa