Filato: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Dan Takarar PRP A Mazabar Jos Ta Arewa

Rahoton dake shigo mana daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar Kotu dake saurarar karararakin zaɓe dake zamanta a kotun High Court 4, Jos a ranar Juma’a ta fitittiki Musa Avia Aggah, dan majalisar wakilan tarayya na jam’iyyar PDP. Musa Avia Aggah ya kasance mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa a majalisar wakilai. Kotun ta bayyana cewa ba Agah bane halastaccen wanda ya lashe zaben fidda gwanin PDP a zaben ba. A hukuncin da Alkalan kotu Justice Hope O. Ozoh. Khadi Usman Umar, da Justice Zainab…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: Dan Luwadi Ya Yi Yunkurin Kashe Kanshi Bayan Shiga Hannu

Rundunan ‘yan Sandan jkhar Adamawa ta kama wani mutum dan shekaru 45 da haihuwa bisa zarginsa da yin luwadi da wani yaro ɗana shekaru goma da haihuwa a Ƙaramar hukumar Mayo Belwa dake jihar. A wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hannun Kakakin rundunar ‘yan Sandan Jihar SP Suleiman Yahaya Nguroje na cewa an samu nasarar kama wanda ake zargin ne biyo bayan kara da Mahaifin yaron wato Akure Usman tare da wasu mutane suka kai ofiahin ‘yan sanda dake Mayo Belwa inda Jami’an ‘yan sandan basu yi…

Cigaba Da Karantawa

2023: Zan Taimaka Wajen Kifar Da PDP – Martanin Wike Ga Shugaban PDP

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnan jihar Ribas Wike ya sha alwashin sa hannu wajen faduwar jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban kasa na 2023. Wike na martani ne game da kalaman da shugaban jam’iyyar PDP ya yi yayin wata hira da BBC Hausa, inda ya ce ”masu kiraye-kirayen ya saukan yara ne da ba su fahimci manufofin kafa jam’iyyar ba”. Gwamna Wike ya kara da cewa ”Na yi tunanin a matsayinka na shugaban jam’iyya wanda ke son jam’iyyarsa ta yi nasarar lashe zabuka, bai…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Sanda Sun Fara Cin Gajiyar Sabon Albashi

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta ce ta fara biyan Jami’an ‘yan sandan kasar sabon tsarin albashi da ta gyara musu. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ranar Alhamis a shafinta na Tuwita. Tun a cikin watan Nuwambar 2020 ne gwamnatin kasar ta yi alkawarin inganta tsarin albashin jami’an ‘yan sandan kasar. Dama dai ‘yan kasar da dama, da ma su kansu ‘yan sandan sun sha korafe-korafen cewa albashin da gwamnatin kasar ke biyansu ya yi…

Cigaba Da Karantawa

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Triliyan 42 – Hukumar Kula Da Bashi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sanarwar da gwamnatin tarayya ta bayar a wannan makon cewa za ta karbo karin bashin naira tiriliyan 11 domin tafiyar da kasafin kudin 2023 ya janyo muhawara a kasar. Dokar harkokin karbar bashi ta nuna cewa karin bashin da Najeriya za ta karbo ya zarta adadin kudin da aka amince ta ranto. Ministar harkokin Kudi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed wadda ta sanar da karbo bashin, ta ce za a karbo bashin ne daga cikin gida da kuma kasashen duniya.…

Cigaba Da Karantawa