Kotu Ta Yi Fatali Da Bukatar Gwamnati Na Mika Kyari Amurka

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya ta yi watsi da ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar ta neman a tasa ƙeyar Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ɗan sandan da aka dakatar saboda zarginsa da karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi zuwa Amurka. Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi fatali da ƙarar da Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya shigar bisa dalilin cewa ƙarar na da naƙasu. A watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta…

Cigaba Da Karantawa

An Sallami Matuka Jirgi Sakamakon Ba Hammata Iska A Sararin Samaniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Paris na ƙasar Faransa na cewa an sallami wasu matuƙa jirgin saman kamfain Air-France biyu sakamakon gwada ƙwanji da suka yi cikin jirgi. Matuƙin jirgin da mataimakinsa sun ba hammata iska yayin da suke tuƙa jirgi ƙirar Airbus A320 daga Geneva zuwa Paris a watan Yuni kamar yadda jaridar Swiss News Outlet ta shaida. Ma’aikatan jirgin sun shiga tsakani inda ɗaya daga cikin ma’aikatan ya tsaya tare da matuƙa jirgin har sai da jirgin ya sauka ba tare da matsala ba. Faɗan nasu dai…

Cigaba Da Karantawa

Tsawaita Yajin Aikin ASUU Ya Haifar Da Rudani A Najeriya

‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da zazzafar muhawara, musamman a shafukan sada zumunta, dangane da tirka-tirkar da a ke yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU, game da kin biyan malaman jami’o’i albashi saboda yajin aikin da suke gudanarwa. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta tsawaita yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar Kungiyar da ke Jami’ar Abuja. Kungiyar ASUU dai ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairu, saboda gaza biya mata tarin bukatunta daga bangaren gwamnatin tarayayyar kasar. Hakan ne ya…

Cigaba Da Karantawa

Kasafin Kudi: Najeriya Za Ta Ciyo Bashin Triliyan 11 A 2023 – Ministar Kudi

Ministar Kudi da tsare-tsaren kasafi Hajiya Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin naira Tiriliyan 11 tare da sayar da wasu manyan kadarorin kasar domin samun kudin da za a cike gibin kasafin kudin shekarar 2023. An ruwaito Ministar na cewa ana sa ran gibin kasafin kudin kasar zai zarta naira tiriliyan 12.42, idan har kasar ta ci gaba ta bayar da tallafin man Fetur a gaba dayan shekarar 2023. Ministar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ta hallara gaban kwamitin kudi na majalisar…

Cigaba Da Karantawa