Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Biya Albashin Watanni Shidda Ba – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ministan ilimi Adamu Adamu ya ce batun biyan malaman jami’o’i albashinsu na tsawon watannin da ba su yi aiki ba shi ne kaɗai abin da ya rage ba a cimma ba a yarjejeniyar ASUU da gwamnati. Minsitan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Sannan Malam Adamu Adamu, ya ce hakkin malaman jami’o’i ne su biya ɗalibai diyya saboda ɓata musu lokacin da suka yi tsawon wata…

Cigaba Da Karantawa

Rikicin Atiku Da Wike Na Neman Cin Kujerar Shugaban PDP

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jigon jam’iyyar PDP, Sam Ohuabunwa ya bayyana cewa ya kamata shugabansu Iyorchia Ayu yayi murabus kan rikicin dan takarar shugaban kasa Atiku da gwamna Wike. Sam Ohuabunwa ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels, A baya shugaban jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya bayyana cewa zai yi mirabus idan har jam’iyyar ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga arewacin Najeriya. Saboda haka ya kamata ya cika alkawarin daya masu yayi murabus tunda ba dan…

Cigaba Da Karantawa

Murnar Cin Jarrabawa: Matasa Sun Nutse A Tekun Legas

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce wasu matasa hudu sun nutse a ruwa a yayin da suke murnar cin jarrabawar kammala sakandire. Lamarin ya afku ne a ranar Talata a tekun Elegushi da ke unguwar masu galihu ta Lekki. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Benjamin Hundeyin, ya wallafa a shafinsa na tiwita cewa matasan sun nitse bayan sun karbi sakamakon jarrabawarsu daga makaranta. Hukumar gudanarwar tekun ta ce mamatan na daga ckin dalibai 10 da suka je wajen don yin murnar samun nasara a jarrabawarsu…

Cigaba Da Karantawa

Cin Zarafin Dan Kallo: ‘Yan Sanda Sun Gargaɗi Ronaldo

‘Yan sanda sun ja kunnen Cristiano Ronaldo, bisa wani faifan bidiyon da ya nuna dan kwallon ya wafce wayar dan kallo ya buga da kasa. ‘Yan Sandan Merseyside sun ce sun yi wa dan wasan mai shekara 37 tambayoyi, sun kuma gargadeshi kan laifin da ya shafi cin zarafi da lalata dukiya. Jami’an tsaron sun tabbatar da faruwar lamarin sun kuma damu da halayar a karawar da United ta yi da Everton ranar 9 ga watan Afirilu. Hukumar kwallon kafa ta Ingila itama ta ce za ta gudanar da nata…

Cigaba Da Karantawa

Tattalin Arzikin Saudiyya Ya Yi Wa Kasashen Duniya Fintinkau

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Washington DC na Ƙasar Amurka na bayyana cewar Asusun bada lamuni na Duniya ya ce da yiwuwar tattalin arzikin Saudiyya zai iya zama mafi habbaka a duniya a wannan shekarar yayin da tattalin azrikin duniyar ke fuskantar koma baya. A cewar Bankin masarautar na duba yadda za ta cimma kashi 7.6, wanda bukatar mai da ake da ita a duniya za ta matukar taimakawa da kuma habbakar bangarorin da ba na mai ba. Karin bukatar da ake da ita ta makamashi – saboda rikicin…

Cigaba Da Karantawa

Dalilin Jefa ‘Yan Najeriya Cikin Duhu – Hukumar Lantarki

Ƴan Najeriya sun auka cikin duhu a sassan ƙasar sakamakon tafiya yajin aikin da ma’aikatan wutar lantarki na ƙasar suka fara. Sun fara yajin aikin ne ta hanyar hana shiga da fita a hedikwatar kamfanin dillancin wutar lantarkin na Najeriya TCN a Abuja, ranar Laraba da safe. Sun fara kashe makunnan lantarki a ofisoshin da ke faɗin ƙasar. Wani jami’in kamfanin ya shaida wa BBC cewa suna fatan gwamnati za ta shiga cikin lamarin, idan ba haka ba kuwa to kowa zai zauna a cikin duhu. Yajin aikin ya samo…

Cigaba Da Karantawa