Tsaro: Kungiyar Matasan Arewa Ta Yi Kiran Buhari Ya Kori Monguno

Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya ta yi kira da babban murya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi hanzarin sallamar mai bashi shawara akan harkar tsaro Janar Monguno wanda shine me ba shugaban ƙasa shawara da akayi wanda yafi kowanne rashin tabuka komai a tsawon shekarun dimokuraɗiyya. A gida a ba tsira ba, a hanya haka, a gonaki, da duka wuraren neman abinci, biyan fansa ya zama kaman ba komai ba, shi saboda yana inda tsaro yake, yasan yan ta’adda basu iya kaiwa gareshi, shi yasa yake yadda ya ga…

Cigaba Da Karantawa

Ketare: An Yi Yunkurin Hallaka Salman Rushdie A Amurka

Rahotanni daga birnin New York na ƙasar Amurka na bayyana cewa wani mutumi ya kai wa shahararren marubucin nan, Salman Rushdie, hari yayin da yake kan dandamali zai yi jawabi a ƙasar Amurka. Marubucin, wanda aka shafe tsawon shekaru ana masa bazaranar kisa saboda ya rubuta wani littafi, ‘The Satanic Verses,’ da ake zargin ya yi batanci ga Annabi SAW, an farmake shi ne a wani gari dake yammacin New York. A wani bidiyo da Aljazeera ta wallafa, ta ce wani mutumi ya yi shigar burtu zuwa kan dandamalin da…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Fashin Jirgin Kasan Abuja Sun Yaudari Gwamnati – Garba Shehu

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar shugaban kasa ta ce, ‘yan ta’adan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa dake jigila daga Abuja zuwa Kaduna sun yaudari gwamnati. Hadimin Shugaban kasa a fanin yada labarai Malam Garba Shehu, ya bayyana haka inda ya shaidawa BBC cewa gwamnatin tarayya ta biya wa shugaban wanda suka yi garkuwa da fasinjoji jirgin kasa bukatarsa amma ya saba alkawari. Garba Shehu yace Shugaban ‘yan ta’addan ya nemi gwamnati ta saki matarsa mai juna biyu kuma bayan haka…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: An Cafke Barayin Da Suka Sace Miliyoyi A Gidan Gwamnati

Rahoton dake shigo mana daga birnin Katsina na bayyana cewar yanzu haka dai wasu jami’ai a ofishin gwamnan jihar na hannun ‘yan sanda bisa zargin satar wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba a ofishin gwamna a daren Lahadi. Majiyoyi sun ce kudin da aka sace sun kai N31m, duk da cewa babban daraktan Gwamna Aminu Masari kan sabbin kafafen yada labarai, Al-Amin Isah, ya ce bai san adadinsu ba. An kuma bayyana cewa an yi satar ne a daren Lahadi a lokacin da ake tafka ruwan sama…

Cigaba Da Karantawa

Matsalar ASUU Za Ta Kare Idan Na Zama Shugaban Kasa – Atiku

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ɗan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce muddin ya zama shugaban kasa, kungiyar malaman jami’a ta ASUU ba za ta sake shiga yajin aiki ba. Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin magana a bikin ranar matasa ta duniya a Abuja ranar Juma’a, inda ya ce mahaifinsa bai so yaje makaranta ba, amma daga baya ya jajirce da kuma shiga makaranta har zuwa matakin jami’a. Wazirin na Adamawa ya kara da cewa hakkin kowane…

Cigaba Da Karantawa

Matsalar Tsaro Na Barazana Ga Najeriya – Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta na barazanar gurgunta shirin aike jami’an tsaro da albarkatun kasa da kuma yanayin tsaro a faɗin kasar. Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin kaddamar da wani daftari na takaita rikice-rikice ta kasa da nufin cike giɓin da aka samu ta hanyar aike jami’an tsaro masu yawa ta hanyar hadin gwuiwa tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati. Shirin da ofishin mai ba shugaban shawara kan…

Cigaba Da Karantawa