Babu Sunan Ahmed Lawan A Sunayen ‘Yan Takara – INEC

Hukumar zabe ta ƙasa (INEC) ta ce ba ta karbi sunayen Shugaban Majalisar Dattawan kasar Ahmed Lawan da tsohon Ministan Harkokin Niger Delta Godswill Akpabio a matsayin ‘yan takarar majalisar dattawa ba. Hukumar ta ce ta ki karbar sunayen mutanen biyu a matsayin dan takara na shiyyar Yobe ta Arewa da kuma na shiyyar Arewa maso Yamma ta Akwa Ibom sakamakon takaddamar da ke tattare da zaben fitar da gwanin da aka ce an zabe su a jam’yyar APC mai mulkin kasar. Da take mayar da martani kan wani rahoto…

Cigaba Da Karantawa

Saudiyya Ta Bada Tallafin Dala Miliyan 10 Ga ‘Yan Gudun Hijirar Ukraine

Gwamnatin Saudiyya ta bayar da taimakon magani da makwanci da ya kai na dala miliyan10 domin ga ‘yan gudun hijirar Ukraine sama da miliyan daya. Shugaban hukumar bayar da agaji a duniya ta kasar Saudiyya wato King Salman Humanitarian Aid and Relief Center (KSrelief), Dr. Abdullah Al Rabeeah shi ne ya sanar da haka a Poland. Ya jaddada kudurin kasar tasa na taimaka wa ‘yan gudun hijirar da suka tsere daga Ukraine zuwa Poland da sauran kasashe makwabta da cewa hakan na daga kudurin kasar na taimaka wa mutanen da…

Cigaba Da Karantawa

Borno: An Yi Nasarar Damke Masu Kai Wa Boko Haram Kayan Abinci

Sojojin Najeriya na bataliya ta 195 sun ce sun kama mutane bakwai masu jigilar kai wa mayakan Boko Haram da masu satar mutane kayayyaki. Hukumomin sojin sun ce sun yi nasarar kama mutanen ne da suka hada da Hadiza Ali da Kelo Abba da Mariam Aji da Kamsilum Ali da Ngubdo Modu da Abiso Lawan da wasu, a wajen babban birnin jihar Borno, Maiduguri. An ruwaito cewa wannan na kunshe ne a wasu bayanan sirri da wani masanin harkokin tsaro Zagazola Makama, ya samu tare da bayyanawa manema labarai. Rahoton…

Cigaba Da Karantawa

Satar Mai: Muna Asarar Dala Biliyan Biyu Duk Wata – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce, tana asarar kusan Dala biliyan biyu kowanne wata saboda satar ɗanyen man da ake yi a yankin Neja Delta. Shugaban kamfanin man NNPC na ƙasa Alhaji Mele Kyari ya bayyana haka lokacin da tawagar ministan mai Timipriye Sylva ta kai ziyara ga gwamnan Delta Ifeanyi Okowa a fadar gwamnatinsa da ke Asaba babban birnin jihar. Kyari ya ce, sakamakon wannan kazamin satar da ke gudana, Najeriya ba ta…

Cigaba Da Karantawa