Adamawa: An Kirayi ‘Yan Najeriya Su Gaggauta Karbar Katin Zabe – Shugaban Gidauniyar Attarahu

An kirayi ‘yan Najeriya musammanma wadanda sukayi rijistan katin zabe da su gaggauta karba katin zabensu domin ganin an samu nasarar yin babban zaben shekara ta dubu biyu ta ashirin da uku mai zuwa. Shugaban gidauniyar Attarahu dake jihar Adamawa Mallam Muktar Dayyib ne yayi wannan kira a zantawarsa da Wakilinmu a Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa. Malam Muktar Dayyib yace ya kamata mutane su sani karban katin zaben yana da matukar muhimmanci wanda hakan zai bada damar zabar shugabanni da suka cancanta in kuma har mutum bai da katin…

Cigaba Da Karantawa

Ci Rani Kasar Waje: Sanusi Ya Shawarci Matasa

Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu, ya yi kira ga matasan Najeriya da su daina barin kasar nan domin neman dama a kasashen waje, a matsayin ‘yan ci rani. An ruwaito cewa Sanusi ya yi wannan kira ne ga matasan yayin da yake jawabi a ranar Lahadi a wani taron wasan kwaikwayo mai taken ‘A Truth in Time’ a Birnin tarayya. Taron wanda ya naqalto rayuwa da gogewar tsohon sarkin, Ahmed Yerima, farfesa ne na fannin wasan kwaikwayo a Jami’ar Redeemer, ya rubuta shi, wanda Duke of Shomolu Productions…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Surukar Sanata

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewa wasu gungun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mutum hudu cikin su har da surukar Sanata mai wakiltar mazaɓar Katsina ta arewa a majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Babba Kaita. Wani mazaunin garin Kankia, Malam Muhammad Sani, ya ce maharan sun farmaki garin ne a farkon awannin ranar Litinin kuma suka ci karen su babu babbaka na tsawon awanni. Ya ce faramakin ya faru ne a Anguwar Bakin Kasuwa, inda yan bindigan suka kutsa kai gidan Mani Babba Kaita, ƙanin…

Cigaba Da Karantawa

Ko Gawata Ba Za Ta Kusanci PDP Ba – Martanin El Rufa’i

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewa Gwamnan Nasiru Ahmad El Rufa’i ya mayar da martani ne ga ikirarin da kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Daniel Bawala, ya yi a shafinsa na Twitter. A baya Bwala ya yi hasashen cewa, Nasiru El Rufa’i wanda tsohon minista ne na babban birnin tarayya Abuja zai fice daga jam’iyyar APC mai mulki nan ba da jimawa ba zuwa jam’iyyar adawa ta PDP. Bwala wanda har a kwanan baya dan jam’iyyar APC ne ya ce…

Cigaba Da Karantawa

Yaki Da Rashawa: Gwamnatin Buhari Ta Saki Manyan Barayin Gwamnati Biyu

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sako wasu tsoffin gwamnoni da aka samu dumu-dumu da laifin rashawa. An sako tsoffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba, wato Sanata Joshua Dariye, da Jolly Nyame daga babban gidan Kurkukun Kuje da ke birnin tarayya Abuja. Wannan na zuwa ne watanni uku bayan afuwar da majalisar kasa karkashin jagorancin shugaban kasar Muhammadu Buhari ta yi a ranar 14 ga Afrilu, 2022. Wata majiya daga gidan Kurkukun ta shaida wa…

Cigaba Da Karantawa