Yajin Aikin ASUU: Zan Kori Dukkanin Malaman KASU – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yayi barazanar sai ya kori duka malaman jami’ar jihar Kaduna KASU, muddin ya bincika ya gano sun shiga yajin aikin da ASUU ke yi. Muryoyi ta ruwaito Gwamnan wanda ke hirar kai tsaye da yan jarida a daren ranar Laraba a Kaduna ya ce a baya ya tsaida albashin ma’aikatan jami’ar amma sai aka shaida masa cewa basu shiga yajin aiki ba “Ma’aikatan jami’ar jihar Kaduna, KASU basu da matsala da Gwamnatin jihar Kaduna domin komi suka nema munyi masu, hakanan duk bukatun ASUU…

Cigaba Da Karantawa

Kyandar Biri: Hukumar Lafiya Ta Kalubalanci ‘Yan Luwadi Su Rage Barbara

Hukumar Lafiya ta Duniya ta shawarci maza da ke neman ‘yan uwansu maza da su rage yawan abokan mu’amular tasu, domin takaita yaduwar cutar kyandar biri. Ta kuma nemi su dinga musayar bayanai game da su. Kashi 98 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar maza ne masu neman maza ‘yan uwansu. WHO ta ce an bayar da rahoton mutum 18,000 a kasashe 78 da suka kamu, galibi a kasashen Turai. An samu mutuwar mutum biyar. Shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce za a iya dakatar da cutar…

Cigaba Da Karantawa

Tsadar Kayan Abinci: Amurka Za Ta Tallafawa Najeriya Da Dala Miliyan 55

Ƙasar Amurka ta sanar da shirin tallafawa Najeriya cikin gaggawa da dala miliyan 55 domin taimaka wa ƙasar wajen shawo kan matsalar tsada da ƙarancin abinci. Wannan wani ɓangaren ne na alkawarin Shugaba Joe Biden a taron G7 da aka gudanar a Jamus, a ƙoƙarin ceto ko kare matalautan ƙasashen daga matsalar abinci da ke addabar duniya sakamakon mamayar Rasha a Ukraine. Amurka ta sanar da wannan shiri ne a wata sanarwa da ofishin jakadancinta a Najeriya ya fitar, inda take cewa waɗannan kuɗaɗe za a bayar da su ne…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Sheikh Abduljabbar

Kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta ƙi amincewa da buƙatar mayar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara zuwa babban birnin tarayya Abuja. Abduljabbar dai ya bukaci kotun da ta mayar da shari’ar tasa zuwa Abuja saboda zargin da yake na cewar kotun Kano ba za ta yi masa adalci ba. A zaman kotun na ranar Laraba ƙarƙashin Mai Shari’a Abdullahi Liman, lauyan Abduljabbar Barista Dalhatu Shehu Usman ya zargi alkalin kotun ta Kano da ganawa da kwamsihinan shari’a Barista Musa Lawan a safiyar ranar gabanin zaman kotun. Sai dai…

Cigaba Da Karantawa

Matsalar Tsaro: ‘Yan Majalisa Sun Yi Yunkurin Tsige Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sanatocin jam’iyyun adawa sun fice daga zauren majalisar dattawan a fusace, bayan da aka yi watsi da kudurin da suka gabatar na tsige Shugaba Buhari. An ruwaito cewa ‘yan majalisar na jam’iyyun adawa sun ba shugaban kasar Muhammadu Buhari wa’adin makwanni shida da ya kawo karshen matsalar tsaro da kasar ke fama da ita. Sun kuma yi barazanar fara batun tsige shugaban matukar ya kasa magance matsalar cikin wa’adin da suka ba shi. Shugaban marasa rinjaye na majalaisar, Sanata Phillip Aduda ne…

Cigaba Da Karantawa