NEMAN AFUWA!!!

A madadin hukumar gudanarwa ta kamfanin ATAR Communications Nigerian Limited mamallakan gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty. Muna neman afuwa dangane da sanya hoton wannan matashi da aka yi a wani labari da jaridar Muryar ‘Yanci mallakar Kamfanin ta yi amfani dashi a ranar 27 ga watan Yunin 2022 mai taken ” Kano: Kotu Ta Haramta Wa Matashi Hawa Doki Na Tsawon Shekaru Uku” Muna neman afuwar amfani da hoton wannan bawan Allah da muka yi ba shine Abdulsalam Bashir ba wanda Kotu ta hana hawa Doki ba. Sanarwa Daga…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Shawarci Musulmi Da Yin Addu’a Domin Nasarar Zaben 2023

A yayin da aka fuskanci Babban zaben shekarar ta 2023 an kirayi al’umma Musulmi da su kasance masu yin addu’o’i a koda yaushe domin ganin an kammala zaben lafiya da cigaban kasa baki daya. Shugabar kungiyar Jama’atu Nasaril Islam bangaren mata dake jihar Adamawa Hajiya Amina Bashir ce tayi wannan kira a wajen adu a ta musamman wanda kungiyar ta shirya a Yola. Hajiya Amina tace shirya irin wadannan addu’o’i yana da mutukan muhimanci don haka ya kamata iyaye su kasance masu shirya addu’o’i da su da yaransu domin neman…

Cigaba Da Karantawa

Abuja: NDLEA Ta Cafke Manyan Dillalan Hodar Iblis

Aƙalla mutum takwas ne hukumar NDLEA mai yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta kama kan zargin safarar hodar-ibilis ko kuma koken. Cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar, kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce wasu daga cikin mutanen da aka kama na yunƙurin fita da ƙwayoyin ne, yayin da wasu kuma ke shiga da su Najeriya. An kama su ne a filayen jirgin sama na Abuja da Legas da Enugu, kuma biyu daga cikinsu mata ne. Ɗaya daga cikinsu mai suna Okwo Paul Okechukwu, an kama…

Cigaba Da Karantawa

Bullar Sabuwar Cuta: NCDC Ta Shiga Bincike

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta ce ta ƙaddamar da bincike kan wata baƙuwar cuta da ta ɓulla a Jihar Delta da ke kudancin ƙasar. Rahotanni na cewa a makon da ya gabata wani ɗalibi ya mutu tare da kwantar da wasu tara a asibiti sakamakon cutar a yankin Boji-Boji na Ƙaramar Hukumar Ika ta Arewa-maso-Gabas. Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter, NCDC ta ce tana sane da wata cuta da aka…

Cigaba Da Karantawa

NEJA: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Ci Rayuka

Rahotanni daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewa mutum ɗaya ya rasu sannan wani ya jikkata bayan kifewar kwale-kwale a Kogin Zumba na Jihar ɗauke da ‘yan kasuwa kusan 50. Mutanen sun fito daga kauyen Shiroro zuwa kasuwar Kwata a Ƙaramar Hukumar ta Shiroro. Rahoton ya ce mutum shida ne kawai aka samu damar cetowa daga fasinjojin da ke cikin jirgin ruwan. Babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Ibrahim Inga, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce bai samu bayanin adadin wadanda abin…

Cigaba Da Karantawa

Tirkashi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Kashe Buhari Da El Rufa’i

A sabon bidiyo da suka fitar ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 a wani jirgin kasa da ke jigila tsakanin Abuja da Kaduna sun yi barazanar sacewa da kashe Shugaba Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Barazanar dai na zuwa ne makwanni bayan da wasu ’yan ta’adda suka kai hari kan tawagar motocin shugaban ƙasa yayin da suke kan hanyar zuwa garin Daura a Jihar Katsina, gabanin tafiyarsa hutun Sallar layya. A cikin bidiyon, ’yan ta’addan sun kuma yi bugun kirjin cewa…

Cigaba Da Karantawa