Har Yanzu Ban Samu Namijin Da Ya Yi Mini Ba – Jarumar Fina-Finai

Fitacciyar jarumar masana’antar Nollywood, Bimbo Akinsanya wacce aurenta ya mutu lokacin tana da yaro mai wata uku a shekarun baya da suka gabata, tace ta mayar da hankali kan fim a yanzu fiye da batun aure. A tattaunawarta da jaridar Vanguard, tace tana kokarin ganin ta ba wa ‘danta lokacinta wanda hakan ke da matukar muhimmanci. Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, ta bayyana yadda take kula da ‘danta ita kadai ba tare da tallafin uban yaron ba. “Ba abun wasa…

Cigaba Da Karantawa

Har Yanzu Korona Na Kisan Jama’a – Hukumar Lafiya

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi gargaɗin cewa jerin waɗanda suka kamu da cutar korona na nuna cewa har yanzu ba a kuɓuta daga annobar ba. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce cutar na ci gaba da yaɗuwa, don haka akwai buƙatar ƙasashe su ɗauki matakan ɗakile ta. Ya ce, ya damu da yadda ake samun ƙaruwar kamuwa da cutar korona. Wannan lamari yana ƙara takura tsarin kiwon lafiya dake cikin matsi, da ma su ma’aikatan lafiyar. Yana jawabi ne a wajen taron kwamitin na WHO, wanda ya yanke hukuncin…

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aikin Malamai: Buhari Bai San Me Yake Ba – Kungiyar ASUU

Ƙungiyar ASUU ta mayar da martani kan kalaman na Buhari, Inda ta ce ta yi mamakin kalaman na shugaban. Farfesa Abdulkadir Muhammad shugaban ASUU shiyyar Kano ya shaida wa BBC cewa ba su ji daɗin kalaman na Buhari ba, yana mai cewa “maganar ta fito ne daga bakin mutumin da kamar bai san abin da ke faruwa ba ko halin da kasa ke ciki.” “A tunaninmu a matsayinsa na shugaban kasa, wannan yajin aikin ba yau muka fara ba, yau an shiga wata biyar, sai muke ganin ƙila ya farka…

Cigaba Da Karantawa