Sukar Atiku: PDP Ta Ba Obasanjo Wa’adin Kare Kai

Babbar Jam’iyyar adawa taPDP, ta bukaci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi karin haske kan kalaman da ya furta kan dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar na cewa ya yi kuskure wurin zabensa a matsayin mataimakinsa a 1999 ba tare da ɓata lokaci ba. A cewar PDP idan tsohon shugaban kasar bai yi karin haske kan kalaman da aka danganta da shi ba cikin awa 48, jam’iyyar za ta fada wa yan Najeriya ainihin ko wanene Obasanjo. Da ya ke magana a taron manema labarai a Kaduna a ranar…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: Umarnin Mallakar Bindiga Ya Haifar Da Cece-Kuce

Shawarar da gwamnatin jihar Zamfara ta yanke ta bai wa dukkan mazauna Jihar damar mallakar bindiga domin kare kansu daga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ta jawo ce-ce–ku-ce. Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da kuma hakan zai ba mutane musamman manoma damar kare kawunansu a lokaci da suke gudanar da ayyukansu. “Hare-haren ta’addanci sun kasance abin damuwa ga jama’a da gwamnatin jiha. Don haka ne, domin mu magance wannan matsala baki daya a yankunanmu, gwamnati ba ta da zabin da ya…

Cigaba Da Karantawa

Dalilin Ficewar Tinubu Kasar Faransa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa domin gudanar da wasu ayyuka, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa, Tunde Rahman, ta bayyana. Tunde ya ce ɗan takarar kuma jagoran jam’iyya mai mulki ba zai jima sosai ba a ziyarar da ya kai birnin Paris. Kafin ya yi balaguron sai da ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja. Sai dai wasu rahotanni da aka fitar a wasu kafofi na…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Ƙungiyar Ansaru Ta Haramta Siyasa

Ƙungiyar Ansaru dake ikirarin kishin addinin Musulunci ta haramta duk wasu al’amura da ke da alaƙa da siyasa a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna. Kungiyar ci gaban Masarautar yankin ta ce yanzu haka kungiyar ta shimfida wasu sharuɗɗa da suka dace da salon shugabancinta, kuma duk wanda aka samu da saɓa su, yana iya fuskantar hukunci mai tsanani. Bayanan da BBC ta tatattara sun bayyana cewa kungiyar ta raba wa jama’a wani saƙo da ke ƙunshe da dukkan manufofinta, ciki har da na kawo ƙarshe dimukradiyya da harkokin siyasa…

Cigaba Da Karantawa

Alkalin Alkalan Najeriya: Tanko Ya Fita Olukayode Ya Shigo

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an rantsar da Mai shari’a Olukayode Arwoola a matsayin muƙaddashin babban jojin kasar. Hakan ya biyo bayan murabus da Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi, mai shari’a Tanko ya yi murabus ne bisa dalili na rashin lafiya. Mai shari’a Olukayode Ariwoola shi ne ke bi wa babban jojin Najeriya Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad baya, kuma tuni ya karbi rantsuwa tare da karɓar ragama a matsayin mukaddasshin babban jojin Najeriya. An wayi gari da labarin murabus din babban jojin Najeriyar, Mai…

Cigaba Da Karantawa