Ta’addanci: Ana Wuce Gona Da Iri Wajen Kama Fulani – Gumi

Da ya ke magana a wurin taron kaddamar da Kungiyar Kare hakkin Makiyaya a Kaduna, Dr Ahmad Gumi ya ce kawo yanzu, akwai matasan fulani da yara da yawa a wadanda ba su ji ba ba su gani ba a tsare hannun jami’an tsaro. Ya ce dalilin kafa kungiyar shine tabbatar da cewa matasan Fulani da ba su aikata komai ba sun samu adalci, ya kara da cewa za ta taimaka wurin kawo zaman lafiya a kasar. “Kwanaki kadan da suka gabata, wani mutum ya kira ni ya ce jami’an…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Unguwannin Cikin Birni

Labarin dake shigo mana daga cikin garin Katsina na tabbar da cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai samame a wasu Unguwannin cikin birnin na Katsina. Wuraren da suka ƙaddamar da harin sun ƙunshi Sokoto Rima wajen Difiri, da bayan KTTV Inda ake kyautata zaton cewa sun Ɗauki Mutane Bakwai tare da tafiya dasu. Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbar da kai harin, Inda ya bayyana cewa Maharan sun kai samame ne da misalin ƙarfe biyu da rabi na…

Cigaba Da Karantawa

Korar Malaman Kaduna: Malamai Za Su Tsunduma Yajin Aiki

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Kaduna ta kori malaman firamare sama 2000 a cikin makon jiya bisa dalilin basu zauna rubuta jarabawar kwarewa da gwamnatin ta shirya ba. Cikin waɗanda aka kora har da Shugaban kungiyar na kasa Mista Amba Audu wanda shima bai zauna rubuta jarabawar ba. Rahotanni sun bayyana Shugaban ƙungiyar ya umarci malamai da su kaurace wa jarabawar saboda babu dalilin sake rubuta irin wannan jarabawa bayan an taɓa rubuta irints a baya. Dalilin haka Shugaban Malaman ya ki rubuta jarabawar da wasu malamai sama…

Cigaba Da Karantawa

2023: Dalilin Da Ya Sa Ban Nemi Yin Tazarce Ba – Buhari

A ranar Alhamis ne mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana manyan dalilan da yasa bai zai sake tsayawa takara karo na uku ba, wato yin tazarce. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi magana ne a taron kungiyar kasashe renon Ingila da ya gudana a ƙasar Ruwanda. An gudanar da taron ne a cigaba da taron Shugabannin kasashen renon ingila wato Commonwealth karo na 26 a birnin Kigali na kasar Ruwanda. Mai girma Shugaban ƙasa ya nanata kudurinsa na mutunta iyakar wa’adin mulkinsa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda…

Cigaba Da Karantawa