Neja: Jama’ar Gari Sun Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar mazauna yankunan da ta’addancin ‘yan bindiga yayi kamari a yankin Kusherki na karamar hukumar Rafi ta jihar sun nemi zaman lafiya da ‘yan bindiga. Rahotanni sun bayyana yadda ‘yan bindigan suka bukaci a yi yarjejeniyar zaman lafiya da mazauna yankin tare da sharadin cewa ba zasu dinga kai su kara wurin hukuma ba duk lokacin da suka ketare yankunansu. Shugaban yankin Kusherki, Alhaji Garba Kusherki, ya sanar da Daily Trust cewa tuni suka tura wakilai domin tattaunawa da ‘yan bindigan.…

Cigaba Da Karantawa

Zargin Cire Sashin Mutum: An Damke Ekweremadu A Birtaniya

Rahoton dake shigo mana daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya na bayyana cewar Hukumomi a kasar sun damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa. Hukumar ‘yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za’a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, kamar yadda jaridar Skynews ta ruwaito. ‘Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo…

Cigaba Da Karantawa

Zargin Tsafi: An Damke Sanata Ekweremadu A Birtaniya

Rahoton dake shigo mana daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya na bayyana cewar Hukumomi a kasar sun damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa. Hukumar ‘yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za’a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, kamar yadda jaridar Skynews ta ruwaito. ‘Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Jami’an Tsaro Sun Tarwarsa Sansanin ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar tawagar hadin gwiwa da ta kunshi rundunar yan sandan Najeriya da yan bijilante a karamar hukumar Safana ta Jihar sun kashe yan ta’adda biyu yayin musayar wuta a kauyen Sabon Dawa. A cewar kakakin yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Laraba, ya ce an yi musayar wutan ne a yammacin ranar Talata, tsakanin ‘yan ta’addan da jami’an tsaro. “A ranar 21 ga watan Yunin 2021 misalin karfe 5 na yamma, an samu…

Cigaba Da Karantawa

Jira Ya Kare: Daliban Jami’a Za Su Koma Darasi – Minista

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan kwadago da samar da ayyuka Chris Ngige ya ce nan bada jimawa ba za a kawo karshen yajin aikin da malaman jami’a ke yi a kasar. Ngige ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taro a fadar Shugaban kasa. Ngige ya musanta zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya na yin ko oho da korafe-korafen ASUU, inda ya tabbatar da cewa suna kan tattaunawa da Shugabancin kungiyar. Ministan ya kara da cewa…

Cigaba Da Karantawa

Sauya Sheka: Abdullahi Adamu Ya Koka Da Yadda Ake Barin APC

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki Sanata Abdullahi Adamu ya ce ya damu matuka, kan yadda ake barin jam’iyyar. Sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga APC zuwa wasu jam’iyyun, bayan sun kasa samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar a zaben 2023. Sanatocin da suka fice daga APCn sun hada da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, da Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi, da Dauda Jika daga jihar Bauchi da kuma Ahmad Babba Kaita daga jihar Katsina. Sauran sun hada da Lawal Yahaya Gamau daga Bauchi, sai kuma Francis Alimikhena daga jihar…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Zai Ziyarci Kasar Ruwanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai halarci taron shugabannin ƙungiyar Commonwealth na ƙasashe rainon Ingila da ke gudana a ƙasar Rwanda daga 20 zuwa 26 ga watan Yuni. Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Laraba ta ce shugaban zai halarci buɗe bikin a hukumance ranar Juma’a. Taron mai laƙabin CHOGM 2022, zai tattauna kan halin rayuwa da kuma ci gaban al’ummar ƙungiyar fiye da biliyan biyu da ke zaune a ƙasa 54 na nahiyoyin Afirka da Asiya da Amurka…

Cigaba Da Karantawa

Yakar Yunwa: Bankin Duniya Zai Ba Afirka Tallafin Dala Biliyan Biyu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Washington DC na ƙasar Amurka na bayyana cewar Bankin Duniya ya amince da tallafin kuɗi na sama da dala biliyan biyu ga ƙasashen Gabashi da Kudancin Afirka, don taimaka musu wajen bunƙasa wadatar abinci. A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce kimanin mutum miliyan 68 a yankin ke fuskantar matsalar ƙarancin abinci da barazanar yunwa. Ya ƙara da cewa matsalolin sauyin yanayi da tabarbarewar tattalin arziki da siyasa da rikice-rikice na kara ƙamari. Yaƙin Ukraine ya ƙara haifar da matsalar ƙarancin…

Cigaba Da Karantawa