Dalilinmu Na Kin Janye Tallafin Fetur – Fadar Shugaban Kasa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce abin da ya sa bai cire tallafin man fetur ba shi ne don gudun tsananta wa al’ummar ƙasar. Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Bloomberg ta intanet ta Amurka da aka wallafa a ranar Talata. Bloomberg ta tambayi Buhari cewa me ya sa ya ƙi amsa kiraye-kirayen da Asusun ba da lamuni na duniya IMF, da Babban Bankin Duniya ke masa tsawon shekaru na ya janye tallafin fetur kuma canjin kuɗaɗen ƙasashen waje su zama…

Cigaba Da Karantawa

Sokoto: ‘Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Maniyyata Aikin Hajji

Labarin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta tabbatar da kai hari kan jerin motocin maniyyata aikin Hajji da suka fito daga karamar hukumar Isa. Maniyyatan suna kan hanyarsu ne ta zuwa garin Sokoto, babban birnin jihar domin tashi zuwa kasar Saudiyya, a lokacin wasu da ake zargin barayin daji ne suka auka wa ayarin motocinsu. Sai dai sanarwar da gwamnatin Sokoton ta fitar ta ce maniyyatan sun isa garin Sokoto lafiya tare da rakiyar jami’an tsaro. A cewar Kamishinan Sadarwa, Isah Bajini Galadanchi, tuni…

Cigaba Da Karantawa

Ku Yi Gaggawar Ceto Sauran Fasinjojin Jirgin Abuja – Buhari Ga Jami’an Tsaro

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Buhari ya umarci jami’an tsaro su sake jajircewa wajen ceto sauran fasinjojin jirgin kasa da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban ya ce, ya yi farin ciki fasinjojin da aka sako, kuma za a ci gaba da kokari wajen ganin sauran mutanen da ke hannun ‘yan bindiga sun dawo gida cikin koshin lafiya. A ranar 28 ga watan Maris din 2022, ‘yan…

Cigaba Da Karantawa

Kisa: Babu Dalilin Cigaba Da Zaman ‘Yan Arewa A Kudu – Mahdi Shehu

Sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahdi Shehu ya koka dangane da halin rashin tabbas da ‘yan Arewa ke shiga a yankin kudancin Najeriya, inda ya yi kira ga a gare su da suyi gaggawar dawowa gida Arewa. Mahdi Shehu ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aike wa ‘yan Arewa mazauna kudanci, inda ya tunatar dasu baiwa da Allah ya yi wa yankin arewa na dukkanin abin da ɗan Adam ke bukata a rayuwa, bisa ga haka su dawo Arewa domin kaucewa halin rashin tabbas…

Cigaba Da Karantawa

2023: Bai Zama Dole Jam’iyyar Labour Ta Dauki Kwankwaso Ba – Sakataren Jam’iyya

Babban Sakataren jam’iyyar Labour na Kasa Alhaji Umar Ibrahim Mai Raƙumi, yace a halin da ake ciki jam’iyyar ta mayar da hankali ne wajen zaɓo mataimaki da zai rufa wa ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Peter Obi baya daga yankin Arewacin kasar. Mai Raƙumi ya ƙara da cewar babu shakka tattaunawa ta yi nisa tsakanin jam’iyyar da ɓangaren tsohon gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, amma hakan ba ya nuna cewar dole ne jam’iyyar sai ta ɗauki Kwankwaso mataimaki ba. Babban Sakataren ya bayyana hakan ne a yayin wata…

Cigaba Da Karantawa