Kotu Ta Hana INEC Dakatar Da Rijistar Katin Zabe

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC dakatar da rajistar katin zaɓe. Hukumar dai ta sanya ranar 30 ga watan Yunin 2022, a matsayin ranar da za ta dakatar da rajistar masu zaben. Sai dai kotun karkashin jagorancin mai shari’a Mobolaji Olajuwon ta bayar da umarni na wucin gadi kan daina yin rajistar har zuwa ranar 29 ga watan Yuni da za ta sake zama domin sauraron karar.…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Ta Fi Karfinka A Yanzu – Babangida Ga Peter Obi

Tsohon gwamnan jihar Neja Alhaji Babangida Aliyu ya bayyanawa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi cewa ba zai iya mulkar Nijeriya a shekarar 2023 ba. Inda yace yayi gaggawa kamata yayi ya bari sai a shekarar 2027 ko kuma shekarar 2031 sai ya nemi takarar shugaban kasar. Babangida ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai na Channels a Abuja, sai dai ya bayyana Peter Obi a matsayin Mutumin kirki. A karshe Babangida yace da ace Peter Obi bai sauya sheka ba da…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta Yi Tir Da Korar Malamai

Kungiyar Marubuta kare hakkokin ɗan Adam ta Najeriya, HURIWA, ta caccaki gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Nasiru El Rufa’i na korar Malaman makarantu da ta yi, inda ta bayyana hukuncin a matsayin daukar fansa ba bisa ka’ida ba, kuma abin Allah wadai . Malaman da aka kora sun hada da shugaban kungiyar malamai ta kasa (NUT) Audu Amba, wanda aka kora bisa zargin kin yin jarabawar cancanta da hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar KADSUBEB ta shirya. HURIWA ta goyi bayan shugaban kungiyar NUT na jihar Ibrahim Dalhatu, wanda…

Cigaba Da Karantawa

Rashin Imani Ne Korar Malamai Da El Rufa’i Ya Yi – Kudan

Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar PDP Isah Ashiru Kudan, ya yi kira ga gwamnan Nasir El-Rufa’i ya dakatar da korar ma’aikatan da ya ke yi a jihar ba tare da bata lokaci ba. Idan dai ba a manta ba, gwamnatin El-Rufai ta kori malaman makarantun firamare, ciki har da shugaban kungiyar malamai ta kasa wanda ɗan asalin jihar Kaduna ne. Isah Ashiru ya soki hakan ne a cikin wani sako da ya fitar, inda ya ce a wannan lokaci da talaka ke hannu-baka-hannu- kwarya bai kamata a ce…

Cigaba Da Karantawa

Da Yiwuwar Ragowar Sauran Fasinjojin Jirgin Abuja Su Mutu – Mamu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Malam Tukur Mamu wanda ya taimakawa gwamnati wurin sasantawa da ‘yan bindiga suka saki mutane 11 cikin waɗanda su kayi garkuwa a harin jirgin kasa na Abuja-Kaduna yace sauran mutanen dake dajin ka iya mutuwa. Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace macizai na cizonsu kuma ba wata cikakkiyar kulawa suke samu ba, kuma yace nan da ‘yan makwanni zasu iya rasa rayukansu saboda rashin lafiya. Mamu wanda ya kasance hadimin Sheki Ahmad…

Cigaba Da Karantawa