Neja: Fasinjoji 18 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota

Labarin dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Fasinjoji goma sha takwas a wata motar bus mai daukar mutane 18 sun kone kurmus a wani hatsarin Mota da ya wakana a Gidan Kwano hanyar Minna-Bida a karamar hukumar Bosso da ke jihar. An tattaro cewa motar ta fito ne daga jihar Lagas zuwa wani wuri da ba a sani ba amma dai hukumomi sun ce ta yiwu tana a hanyarta ta zuwa Kano ko jihar Sokoto. Hatsarin wanda ya afku da misalin karfe 3:00 na…

Cigaba Da Karantawa

An Kakaba Wa Kamfanonin Jiragen Ƙetare Takunkumi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta hana kamfanonin sufurin jiragen sama na ƙasashen waje taɓa kuɗaɗensu da suka kai dala miliyan 450. Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa hukumomin Najeriya, ƙasar da ta fi saura girman tattalin arziki a Afirka, sun dakatar da fitar da kuɗaɗen ƙasar waje don sayo kaya da kuma na masu zuba jarin da ke son kai wa ƙasashensu na asali. Gwamnati ta ɗauki matakin ne saboda ƙarancin kuɗaɗen ƙasar waje da ƙasar ke fuskanta, musamman na…

Cigaba Da Karantawa

Borno: Mayakan ISWAP Sun Yi Wa Soji Ta’adi

Ƙungiyar mayaƙan ISWAP mai iƙirarin jihadi ta yi iƙirarin cewa ta kashe mayaƙan sa-kai uku da ke aiki da rundunar sojan Najeriya a Jihar Borno. Kazalika, ta ce ta yi garkuwa da wasu ma’aikatan agaji na ƙungiyar Red Cross yayin harin da ta ce ta kai ranar Juma’a. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne ciikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na dandalin Telegram ranar Asabar, tana mai cewa ta kai harin ne a garin Monguno. A watan Agustan 2020 ne ƙungiyar ta ayyana yaƙi a kan ma’aikatan agaji da…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: El Rufa’i Ya Kori Malamai 2,357 Daga Bakin Aiki

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar hukumar Ilimi bai ɗaya ta Jihar Kaduna, KADSUBEB, ta ce ta kori malamai 2,357 wadanda suka fadi jarrabawar cancanta da aka gudanar a baya-bayan nan Mai magana da yawun hukumar, Malama Hauwa Mohammed cikin wata sanarwa da ta fitar, a ranar Lahadi a Kaduna ta ce hukumar ta yi wa fiye da malamai 30000 gwajin cancantar a watan Disambar 2021. Ta ce an kori malamai 2,192 na Firamare ciki har da shugaban kungiyar malamai na kasa, NUT, Mr Audu Amba,…

Cigaba Da Karantawa

Zaben Ekiti: Manuniya Ce Ta Nasarar APC A 2023 – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhamadu Buhari, ya yi wa zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Ekiti a ƙarƙashin Jam’iyyar APC murnar lashe zaɓen gwamnan jihar. A wani saƙon da Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya buƙaci duka Ƴan Jam’iyar APC a ciki da wajen Najeriya da su kalli wannan zaɓen a matsayin manuniyar nasarar APC a zaɓen 2023. Shugaba Buhari ya yaba wa Biodun Oyebanji kan nasarar da ya samu a zaɓen inda ya ce ya cancanci ya zama gwamna sakamakon irin gudunmawar da…

Cigaba Da Karantawa