Yobe: Sunan Shugaban Majalisa Ya Bayyana A Jadawalin INEC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa an bayyana sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa na jam’iyyar APC a zaben 2023. Lamarin na zuwa ne ‘yan awanni bayan Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na kujerar, ya jadadda cewa ba zai janyewa shugaban majalisar dattawan ba. Lawan dai ya yi takarar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar APC sannan awanni kafin fara zaben fidda gwanin sai shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu ya sanar da shi…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: An Bada Hutun Kwanaki 5 Domin Rijistar Zabe

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta ba ma’aikatan jihar hutun mako ɗaya domin su yi rajistar katin zaɓe da ake gudanarwa yanzu haka a faɗin ƙasar. Matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamashinan Yaɗa Labarai na Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar a yau Asabar. Ya ce Gwamna Bello Matawalle ya amince da ba da hutun ne daga Litinin, 20 zuwa 24 ga watan Yuni. “Sakamakon wannan sanarwa, an umarci dukkan kwamashinoni da masu bai wa gwamna shawara da…

Cigaba Da Karantawa

2023: Da Yiwuwar Mu Hade Da Jam’iyyar Labour – Kwankwaso

Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa na tattaunawa da jam’iyyar Labour kan yiwuwar kafa kawancen hadin gwiwa a zaɓen baɗi. “Gaskiya muna tattaunawa da Peter Obi kuma an kafa wani kwamiti da ya ke aiki don duba yadda za a yi ƙawancen a tsakaninmu. “Tabbas ƴan uwa da abokan arziki na ta zarya domin tattaunawa kan shirin haɗewar,” in ji Kwankwaso. “ƙawancen na da muhimmanci domin kamar yadda ku ke gani jam’iyyar APC da kuma jam’iyyar ta PDP ba su zabi ‘yan takarar su…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Yi Wa Kasa Dabaibayi Muddin ASUU Ba Ta Janye Yajin Aiki Ba – Dalibai

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar reshen ɗalibai na Gamayyar Ƙungiyoyin Farar hula na Arewa, CNG-SW sun yi barazanar rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin ƙasa da manyan titunan Arewa in har gwamnatin tarayya da ASUU ba su sansata an janye yakin aikin da suke yi ba. Ɗaliban sun kuma yi barazanar rufe ofisoshin jam’iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewacin Nijeriya. Ƙungiyar ta yi wannan barazana ne a wata takardar bayanin bayan taro, wanda Kodinetocin kungiyar na jihohi 19 su ka gudanar ranar…

Cigaba Da Karantawa