Rikicin Kabilanci: Rundunar ‘Yan Sandan Adamawa Ta Cafke Mutum Shida

A kokarin ta na maido da zaman lafiya biyo bayan rikicin kabilanci da aka yi a kananan hukumomin Lamurde da Guyuk a jihar Adamawa, yanzu haka rundunan lyan sandan jihar tana tsare da mutane shida wadanda ake zargi da hannu a rikicin. Kakakin rundunan ‘Yan sandan jihar SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Yola. SP Suleiman yace mutane shida da ake zargin suna taimakawa rundunar da wasu bayanai da zai taimaka wajen kama duk wanda…

Cigaba Da Karantawa

Tsadar Mai: Gidajen Yada Labarai Na Fuskantar Durkushewa – Ramalan

Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Gidajen yaɗa labarai masu zaman kansu na ƙasa Dr Ahmed Tijjani Ramalan yace gidajen Talabijin da Rediyo masu zaman kansu a kasar na fuskantar barazanar daukewa dalilin tsadar man dizel. Ya kara da cewar gidajen Talabijin da Rediyo suna cikin mawuyacin hali biyo bayan halin da suka tsinci kansu na tashin gwauron zabo na abubuwan da suke bukata tun daga kan mai har ya zuwa sauran abubuwan da suke bukata na kuɗade domin biyan tauraron dan Adam. Ramalan ya yi kira da babbar murya ga shugaban kasa…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Atiku Ya Zabi Okowa Mataimaki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Atiku Abubakar ɗan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP, ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai gabatowa. Kwamitin gudanar da ayyuka na jam’iyyar PDP a ranar Laraba ya zabi Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, a matsayin wanda zai kasance mataimakin ɗan takarar shugabancin kasar Atiku. Wasu manya a PDP an gano ba su aminta da Wike ba saboda tsananin kusancin mataimakin shugaban kasa da kujerar shugabancin Kasar. Atiku ya sanar da…

Cigaba Da Karantawa

2023: Hamza Al-Mustapha Ne Mafita A Najeriya – Matasan Najeriya

Gamayyar Kungiyar Matasan tarayyar Najeriya ta bayyana cewar ko shakka babu tsohon Dogarin marigayi Tsohon Shugaban ƙasa Marigayi Sani Abacha Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya shine mafita wanda zai iya ceto kasar daga halin da take ciki idan aka zaɓe shi Shugabàn ƙasa. Kungiyar Matasan ta yi wannan kiran ne a yayin wani taron manema labarai da ta kira a garin Kaduna. Da yake jawabi a yayin taron shugaban gamayyar Kungiyar Matasan Najeriya na kasa Alhaji Abdullahi Abubakar Wali ya bayyana cewar Najeriya ta kama hanyar rugujewa kuma tabbas ana…

Cigaba Da Karantawa

Da Yiwuwar Cin Biredi Ya Gagari Talaka – Masu Gidan Biredi

Shugaban masu gidan burodi a Abuja, babban birnin tarayya Alhaji Ishak Aldul-Rahim ya ce yanzu haka tsadar man dizel ta sanya su cikin mawuyacin hali. Ya ce “Shekaran jiya na sayi man dizel a kan Naira ɗari takwas da talatin kan kowace lita amma daga baya na koma an ce ya zama Naira dubu ɗaya da ɗari biyar kan kowace lita, ban san yadda za mu ƙare ba,” in ji shi, a hirarsa da BBC. Baya ga haka nan ya ce man na dizel yana ƙaranci a wuraren sayarwa. A…

Cigaba Da Karantawa

Hajjin Bana: Sama Da Mahajjata Dubu 100 Sun Isa Saudiyya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya na bayyana cewar fiye da maniyyata 100,000 daga sassan duniya sun isa kasa mai tsarki domin gudanar da aiki Hajjin bana. Hukumomin Saudiyya ne suka bayyana haka cikin wata sanarwar da ta fitar a shafin Haramain Sharifain da ke Tiwita. Sanarwar ta kara da cewa akasarin maniyyatan sun isa birnin Madinah ne.

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aikin ASUU Abu Ne Mai Daure Kai – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin ta shaida wa ‘yan kasar cewa batutuwan da ke tare da yajin aikin da malaman jami’o’in kasar ke yi masu matukar sarkakiya ne. Kungiyoyin malaman jami’a da wasu kungiyoyi uku na ma’aikatan jami’o’i sun tsunduma cikin yajin aiki, inda gwamnatin kasar ta shafe shekara tana tattaunawa da kungiyoyin domin samar da mafita, kamar yadda ministan yada labarai Lai Mohammed ya sanar. Kungiyar malaman jami’a, ASUU ta fara yajin aiki ne daga ranar 14 ga watan Fabrairu kan wasu…

Cigaba Da Karantawa

Muna Dab Da Sanar Da Sunan Mataimakin Atiku – PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ce za ta sanar da sunan wanda zai yi takarar mukamin mataimakin shugaban kasa ga Atiku Abubakar nan da ‘yan sa’o’i masu zuwa. Sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar, Debo Ologunagba ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyar na bin tsarin demokradiyya ne wajen zabo mutumin da zai karbu ga ilahirin ‘yan jam’iyyar da ma ‘yan kasar. Sai dai kakakin ya ki fadin yawan mutanen da kwamitin Chief Tom Ikimi zai tantance. Ya ce: “Ba ni da alkaluman yawan wadanda za a tantance…

Cigaba Da Karantawa

Tsaro A Kaduna: Sha’aban Ya Bukaci Musulmi Da Kirista Su Dauki Azumi

Mai girma Ɗan Buran Zazzau Alhaji Muhammad Sani Sha’aban ya yi kira da babbar murya ga jama’ar jihar musulmi da kirista cewa, kowa ya tashi da azumi a ranar Litinin mai zuwa domin kai kuka ga Allah ya kawo sauki dangane da matsalar tsaro dake addabar Jihar. Sha’aban ya yi wannan kiran ne a wani muhimmin sako da ya aikewa jama’ar Jihar akan mawuyacin halin da Jihar ta tsinci kanta a ciki. Basaraken wanda a hannu guda ya nemi takarar Kujerar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC, ya ce kiran…

Cigaba Da Karantawa