PDP Ta Kafa Kwamitin Nema Wa Atiku Mataimaki

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kafa kwamitin da zai yi aikin nemo wa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, mataimaki. Makwannin da suka wuce ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya lashe zaben fid da gwani, a matsayin wanda zai yi wa PDP takara a babban zaben 2023. Shugaban jam’iyyar Sanata Iyorchia Ayu ne ya kaddamar da kwamitin a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja ranar Talata. Mataimakin Shugaban jam’iyyar shiyyar Arewaci Ambasada Umar Damagum ne zai jagoranci kwamitin, a daidai lokacin da hukumar zabe wato INEC ke dakon a…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ke Jan Ragamar Najeriya Babu Katsalandan – Fadar Shugaban Ƙasa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta fitar da sanarwar da ke cewa shugaban na daukar matakan siyasa a ƙashin kansa, ba tare da katsalandan daga mutanen da ake tunanin suna juya gwamnati ta bayan fage ba da ake kira ‘Cabal’. Sanarwar na dauke ne da sa hannun mataimaki na musamman ga shugaba kan yada labarai Malam Garba Shehu. Wani bangare na sanarwar ya ce ”Shugaba Buhari na daukar matakansa ne kuma ya aiwatar da su ba tare da tsoma baki daga wasu…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Dage Dokar Hana Walwala A Yelwa

Daga Adamu Shehu BAUCHI Biyo bayan samun rahotanni zaman lafiya a cikin anguwan Yelwa da kewaye, Rundunar Yan’sandan Jihar Bauchi ta dage dokar hana yawo a yankin Yelwa da kewaye baki daya dake cikin karamar hukumar Bauchi da sanyin safiyar Talatan nan 14 ga watan Yuni na shekarar 2022. Sanarwar ta fito ne daga hannun Kakakin Rundunar yan’sandan ta Jihar Ahmed Wakil dauke da sa hannun shi a madadin kwamishinan Yan’sandan Jihar Umar Mamman Sanda Sanarwar ta Kara da cewa kwamishinan Yan’sanda yanzu an samu natsuwa da zaman lafiya a…

Cigaba Da Karantawa

2023: Tabbas Tinubu Ne Shugaban Kasa – Kingibe

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne shugaban kasar Najeriya na gaba a babban zaben da za a yi na shekarar 2023. Bola Tinubu dai shine ya yi nasarar lashe tikitin takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC mai mulki a zaben fidda gwaninta da ya gudana a Eagle Square a ranar Laraba, 8 ga watan Yunin shekarar da muke ciki. Jigon na APC kuma babban jagoran Jam’iyyar ya samu kuri’u 1,271 inda ya kayar da sauran abokan karawarsa su…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Jami’an Tsaro Sun Tarwarsa Garken ‘Yan Bindiga

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar haɗakar rundunar jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile harin yan bindiga a kan babbar hanyar Kaduna-Abuja a ranar Lahadi. Dakarun Operation Puff Adder na hukumar yan sanda da haɗin guiwar rundunar Operation Thunder Strike na hukumar sojin Najeriya sun fatattaki yan bindigan tare da halaka wasu a sananniyar hanyar. Kakakin hukumar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige, a wata sanarwa, ya ce Dakarun tsaron sun tari yan ta’addan a yankin, inda suka yi musayar wuta. Sakamakon haka, jami’an…

Cigaba Da Karantawa

Takara: Wankin Hula Zai Kai Ahmed Lawan Dare

Idan ba a manta ba Sanata Ahmed Lawan shugaban majalisar Dattawa ya fafata a zaɓen fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC rabar 8 ga watan Yuni. Kafin zaɓen an yi masa kyakyawar zaton cewa shina jam’iyyar ta ke so ta tsayar ɗan takarar ta amma kuma hakan bai yiwu ba. An ruwaito cewa wanda yayi nasara a zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Bashir Machina ya ce ba zai sauka daga kujerar takara ba.

Cigaba Da Karantawa

Za A Afka Cikin Yunwa Da Wahalar Rayuwa A Najeriya – Bankin Duniya

Babban Bankin Duniya ya yi hasashen cewa ƴan Najeriya da Angola za su fuskanci ƙarin tsanani na hauhawar farashi da rashin wuta da rashin fetur da kuma ƙarancin abinci. Waɗannan matsaloli za su zo ne a yayin da farashin ɗanyen fetur ya kai dala 120 duk ganga ɗaya, lamarin da ake sa ran zai amfani waɗannan ƙasashen da dama su ne manyan ƙasashen Afirka da suka fi samar da fetur. A wani rahoto da Babban Bankin Duniya ya fitar a ƙarshen mako, ya ce “A ƙasashen kudu da hamadar Sahara…

Cigaba Da Karantawa

Shugabancin Kasa: Hatsari Ne Yin Tikitin Musulmi Da Musulmi – Masu Ruwa Da Tsaki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC sun yi kira ga shugabancin jam’iyyar da Kungiyar Progressive Governors da su tsaya neman mataimakin ‘dan takarar shugabancin kasa kan Kiristocin arewa kawai. Hakan ya biyo bayan cece-kuce da ya yi yawa kan tikitin Musulmi da Musulmi wanda ya janyo maganganu daban-daban a kwanakin da suka gabata. A yayin jawabi a wani shiri na shagalin bikin ranar damokaradiyya, Shugaban Kungiyar masu ruwa da tsakin APC na kasa, Aliyu Audu, ya bayyana bukatar watsi…

Cigaba Da Karantawa