Da Dumi-Dumi: An Kona Mai Zagin Annabi Kurmus A Abuja

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu fusatattun matasa sun hallaka wani dan kungiyar Bijilante kan zargin kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW). An tattaro cewa an hallaka dan Bijilantin ne a sashen ‘yan Timba dake kasuwar kayan itace a unguwar FHA Lugbe dake garin na Abuja. Shaidun ganin da ido sun bayyana cewar dan Bijilantin Musulmi ne kuma ya shahara da zagin manzon Allah amma yayi wani sabo a daren jiya washegarin ranar da za a kashe shi. Bayan kalaman batancin, sai ya gudu…

Cigaba Da Karantawa

2023: Takarar Atiku Ta Firgita APC – Waziri

Wani jigo a cikin dattawan babbar jam’iyyar hammayya ta PDP Alhaji Adamu Maina Waziri ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta tsorata da dan takarar da suka fitar shi ya sa take kwan-gaba-kwan-baya wajen fitar da dan takararta na zaben 2023. A hirarsa da BBC Alhaji Maina Waziri ya yi zargin cewa tun da farko ma APC ce ta yi manakisa har hukumar zaben kasar t kara wa’adin sati daya na zaben fitar da dan takara bayan su sun riga sun shirya gudanar da zabensu a lokacin. Tuni dai babbar…

Cigaba Da Karantawa

Hajjin Bana: Za A Fara Jigilar Alhazzan Najeriya Makon Gobe

Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa insha Allahu jirgin farko da zai kwashi kashin farko na mahajjatan bana zai bar Najeriya zuwa Saudiyya mako mai zuwa, hukumar ta sanar da cewa za’a fara jigilar mahajjatan bana 2022 daga Najeriya a ranar 9 ga watan Yuni, 2022. Da yake jawabi yayin sanya hannu kan yarjejeniya da kamfanonin da zasu yi aikin a Abuja ranar Jumu’a, shugaban NAHCON, Zikirullah Hassan, ya ce sun zaɓi ranar ne domin kammala duk wasu shirye-shirye. Ya kuma bayyana cewa sun zaɓi kamfanonin jiragen sama…

Cigaba Da Karantawa

Badakala: An Yi Wa Tsohon Gwamnan Zamfara Hisabi

Rahotannin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar binciken da hukumar EFCC take yi ya bankado wasu akalla Dala $700, 000 da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul-aziz Yari ya kashe daga cikin Naira biliyan 20 da ya karba wajen zuwa kasar Saudi Arabia. Rahoton ya ce babban ‘dan siyasar ya karbi wadannan makudan kuɗaɗen ne daga wajen Akanta Janar ya tafi Umrah da su, Yari ya dauki hadimansa zuwa ketare inda aka kashe kudin. Wani wanda ya san halin da ake ciki, ya shaidawa majiyar mu cewa wadannan kudi da…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Fashewar Gas Ya Jikkata Mutum 70

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar wata tukunyar gas ta sake fashewa ranar Juma’a a unguwar Sharada ‘yan tagwaye inda ta jikkata mutane da dama. Rahotanni sun ce da misalin karfe uku na yammacin Juma’ar ne wasu masu aiki walda da suke kokarin fasa tukunyar gas ne suka fasa wata tukunya, abin da ya janyo fashewarta da ta wasu tukunen gas da ke kusa. Wani wanda abin ya faru a kan idonsa da ake kira Ibrahim Muhammad ya ce “tukunyar gas takwas aka kawo wajen masu…

Cigaba Da Karantawa

Shugabancin Kasa: Gwamnoni Sun Nuna Goyon Baya Ga Osinbajo

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnonin jam’iyyar APC da dama ne aka hango a fadar shugaban kasa inda suka gana da Osinbajo da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Gambari, lamarin da ake ganin cewa ka iya zama wani yunkuri na samun amincewar dan takarar shugaban kasa na sulhu. Rahotannin sun ce da alama akasarin gwamnoni 22 da ke karkashin jam’iyya mai mulki sun amince da goyon bayan takarar Osinbajo, gabanin zaben-fidda gwani. Gwamnonin sun gudanar da tarurruka da dama a masaukin Gwamnan Jihar…

Cigaba Da Karantawa

Shugabancin Kasa: Gwamnoni Sun Nuna Goyon Baya Ga Osinbajo

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnonin jam’iyyar APC da dama ne aka hango a fadar shugaban kasa inda suka gana da Osinbajo da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Gambari, lamarin da ake ganin cewa ka iya zama wani yunkuri na samun amincewar dan takarar shugaban kasa na sulhu. Rahotannin sun ce da alama akasarin gwamnoni 22 da ke karkashin jam’iyya mai mulki sun amince da goyon bayan takarar Osinbajo, gabanin zaben-fidda gwani. Gwamnonin sun gudanar da tarurruka da dama a masaukin Gwamnan Jihar…

Cigaba Da Karantawa