Abuja: An Bukaci Mata Su Tabbata Sun Yi Katin Zabe

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa. A dai dai Lokacin da Jamiyyun Siyasa a Nijeriya ke ci gaba da Kokarin ganin sun fitar da ‘Yan Takarar Kujerun Mukaman Siyasa Daban-Daban a Kasar, Ita Kuwa Shugabar Mata ta Jam’iyyar NNPP Mai alamar kayan Marmari A Babban Birnin Tarayya Abuja, kira tayi ga ‘Yan Uwanta Mata Su Tabbatar sun Mallaki Katin Zabe. Hajiya Saudatu Abdullahi tayi Wannan Kirane a lokacin da take Zantawa da Manema Labarai a Abuja. Saudatu Abdullahi ta ce, Babu Shakka an tafi anbar Mata a baya Musamman a wannan…

Cigaba Da Karantawa

Ilimi: Gwamnatin Gombe Ta Yi Rawar Gani – Kwamared Sabo

Tsohon Shugaban Kungiyar ɗalibai ‘yan asalin jihar Gombe na kasa Kwamared Sani Sabo yace nasarorin da gwamnatin jihar ta ke samu a bangaren ilimi musamman ma wurin gina ƙarin sabbin azuzuwa domin samar da kyakyawan yanayin koyon karatu abu ne dake inganta ilimi daga tushe. Kwamared Sani Sabo wanda ke tsokaci akan bunƙasar ilimi a jihar a hirarshi da wakilinmu, yace an samu cigaba matuka a bangaren ilimi daga tushe a jihar lura da gina sabbin azuzuwa da dalibai ke shiga suyi karatu a natse, musamman a yankunan karkara. Kwamared…

Cigaba Da Karantawa

Badakalar Akanta Janar: Laifin Buhari Ne – Buba Galadima

Tsohon na hannun daman Shugaba Buhari kuma tsohon Mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar APC Injiniya Buba Galadima, ya yi Alla-wadai da yadda ake sama da fadi da kudin kasa karkashin Shugaba Muhammadu Buhari. Galadima ya ce kama Akanta Janar, Ahmed Idris, wanda ake zargi da satar N80bn alama ce babba dake nuna gazawar gwamnatin Buhari mai ikirarin yaki da cin hanci da rashawa. Dattijon ya bayyana hakan ne a hirarsa da tashar ChannelsTV. Yace: “Shin wai kun yarda mutumin nan na yaki da rashawa ya sa aka kama Akanta-Janar?…

Cigaba Da Karantawa

2023: Atiku Ya Daina Yaudarar Kanshi – Kwankwaso

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya ce Atiku Abubakar ya mance da zancen zai iya samun kuri’u miliyan 11m a 2023. Kwankwaso ya ce ya kamata ace tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ankara da cewa siyasar Najeriya ta canza salo a shekaru uku da suka gabata, ta wuce da tunanin shi. Jagoran jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta ƙasa ya yi wannan furucin ne ranar Talata a Abuja, jim…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Sha’aban Ya Yi Sulhu Da Uba Sani

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani ya yi sulhu da abokin takarar sa da ya kada a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC Honarabul Sani Shaaban. Idan ba a manta Sanata Uba Sani ya lallasa Shaaban da kuri’u sama da 1000 in da Sha’aban ya samu kuri’u 16 kacal, sai dai kuma bayan zaben, Sha’aban ya bayyana cewa bai yarda da sakamakon zaben ba. Hakan ya sa da yawa daga cikin masu yin sharhi akan zaben…

Cigaba Da Karantawa

2023: Tambuwal Da Bala Sun Canza Taku

Bayan da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa suka gaza kai bantensu a neman takarar shugaban ƙasa musamman a jam’iyyar PDP yanzu haka sun koma neman wasu kujerun da ba su kai waccan daraja ba. Cikin irin waɗannan ‘yan siyasa akwai gwamnan jihar Bauchi, wanda a yanzu ya koma neman takarar kujerar da yake kai, bayan wanda ya samu takarar gwamman jihar ya janye aniyarsa. A jihar Sokoto ma da akwai irin wannan magana, inda gwamnan jihar da ya nemi takarar shugaban kasa zai koma neman kujerar sanata.

Cigaba Da Karantawa

Babu Cigaban Da Za A Samu A Najeriya Nan Da Shekaru 4 Sai Bashi – Bankin Duniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Bankin Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya yi gargaɗi ga Gwamnatin Najeriya cewa idan ba ta tashi tsaye ba, to babu makawa nan da shekarar 2026 kuɗaɗen haraji da sauran kuɗaɗen shiga zai riƙa tafiya wajen biyan basussukan da gwamnatin ƙasar ta ciyo ne. Wakilin IMF a Najeriya Ari Aisen ne ya bayyana haka a cikin wani rahoton da ya fitar ranar Litinin a Abuja. Bayanin dai ya na ƙunshe ne a cikin Rohoton Halin da Tattalin Arzikin…

Cigaba Da Karantawa