Dan Bindiga Ya Fi Deligate Imani – Shehu Sani

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya ce babu maraban ƴan bindiga da ‘Deliget’ a siyasan Najeriya. Shehu Sani ya bayyana cewa yadda mahara ke karɓar kuɗi a hannun waɗanda suka yi garkuwa da haka suma ‘Deliget’ ke karvar irin wannan kuɗade a hannun mutane da sunan wai za su zabe su. ” Na shiga siyasa ne domin a gyara tsarin a tsaftace shi ta yadda za a rika zaɓen nagartattun mutane waɗanda suka cancanta ta hanyar yin zaɓen mai aminci da nagarta tun daga zaɓen ƴan takara…

Cigaba Da Karantawa

Za A Kashe Miliyan 999 Wajen Ciyar Da Dalibai – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta riƙa kashe naira miliyan 999 a kullum wajen ciyar ‘yan makarantar firamare miliyan 10 a kowace rana a shirin ta na ciyar da ɗalibai, wato ‘National Home Grown School Feeding Programme’ (NHGSFP) da ta ke gudanarwa a duk faɗin ƙasar nan. Shugabar gungun ma’aikatan da ke gudanar da shirin, Hajiya Aishatu Digil, ita ce ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki da aka yi kan hanyoyin rarraba abincin da sake duban fasalin kuɗin…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: Yari Ya Yi Amai Ya Lashe

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Zamfara na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Alhaji Abdulaziz Yari, ya ba da umarnin gaggawa na janye kara uku da ya shigar da shugabancin jam’iyyar APC. An ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan sulhun da aka yi tsakanin ɓangarorin APC biyu na Zamfara masu adawa da juna. Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sasanta tsagin Gwamna Bello Matawalle da tsagin tsohon gwamna Yari da Sanata Kabiru Marafa a kwanakin baya. Wannan sulhu da aka samu tsakanin ɓangarorin ya bude sabon shafi…

Cigaba Da Karantawa

Dalilina Na Watsi Da Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa – Zulum

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan Babagana Umara Zulum ya lashe zaben fidda gwanin jihar da aka yi, ya kuma yi watsi da masu yi masa ta yin ya nemi mataimakin shugaban Najeriya. Babagana wanda shi kadai ne dan takarar a karkashin jam’iyyar APC ya lashe zaben ba tare da hamayya ba, wanda hakan zai ba shi damar karawa da takwarorinsa na sauran jam’iyyun a zaben 2023. An yi zaben fidda gwanin ne a cibiyar wasanni ta El-Kanemi da ke Maiduguri a…

Cigaba Da Karantawa

Abin Kunya Ne Yadda Zabukan Fidda Gwani Suka Kasance – Jonathan

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi Allah wadai da zaben fidda gwani da jam’iyyu ke yi a kasar nan. Da yake bayani a Abuja a ranar Alhamis wajen kaddamar da wani littafi mai suna “Political Party Governance” wanda Dr Mohammed Wakili tsohon ministan lantarki a lokacin Jonatha ya rubuta, ya ce abin kunya ne ka ba wakilai kudi su zabe ka, bayan ka fadi kuma ka ce su mayar maka da kudinka. Ya kara da cewa “Duka zabukan da…

Cigaba Da Karantawa