Taraba: Mafusata Sun Yi Wa Shugaban APC Dukan Kawo Wuka

BASHIR ADAMU, JALINGO Rahotannin dake zuwa mana yanzu daga Jalingo babban birnin jihar Taraba na cewa ana zargin wasu mafusatan Matasan APC sun lakadawa Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Taraba, Barista Ibrahim Tukur El-Sudi dukan kawo wuka, jim kadan bayan kammala ganawar sirri na masu ruwa da tsaki a zaben fidda gwani na Gwamna a Jam’iyyar. Rahoton ya kara da cewa hakan ya biyo bayan wasu makudan kudade ne da Matasan suka gani makare a cikin Motar Shugaban Jam’iyyar da suke zargin cewa kudaden cin hanci ne ya karba a…

Cigaba Da Karantawa

Taraba: PDP Ta Yi Tuwona Maina A Zaben Fidda Gwani

BASHIR ADAMU, JALINGO Rahotannin dake zuwa mana daga Jihar Taraba na cewa anyi tuwona maina a zabubbukan fidda gwani na ‘yan-takaran da za su wakilci Jam’iyyar PDP a zaben shekara 2023. Inda Shugaban Jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Taraba, Laftanal Kanar, Agbu Kefas, mai Ritaya, wanda tun a farko ake zargi da cewa shine dan-takaran da jigo a Jihar ta Taraba, Janar T.Y. Danjuma mai Ritaya, ya kakaba musu duk da cewa Jam’iyyar Jihar basu aminta da dan takaran ba, ya lashe zaben fidda gwani na Gwamna da kuri’u…

Cigaba Da Karantawa

Gombe: Gwamnati Ta Share Wa Al’ummar Herwagana Hawaye

Al’ummar Unguwar Herwagana dake garin Gombe sun cika da murna tare da bayyana farin cikin su bisa kawo musu dauki da gwamnatin jihar tayi wurin gyara musu kwari da ya dade yana addabar su, wanda yake silar janyo rushewar gidaje. A wata ziyarar gani da ido da gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya ya kai inda ake gudanar da aikin ya bayyana jin dadi da yadda yaga aikin ke gudana,yana mai cewa aikin wani kokari ne na gwamnatin shi wurin kyautata rayuwar al-umma. Hakanan gwamnan ya kuma duba aiki hanya da…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Kungiyar ‘Yan Jarida Za Ta Kaurace Wa Taron PDP

Kungiyar ‘yan Jarida ta ƙasa reshen Jihar Kaduna ta yi kira da babbar murya ga jam’iyyar PDP da ta gargadi jami’in yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar Kaduna Katoh Alberah a ƙoƙarin da yake yi na raba kawunan ‘yan Jarida a jihar. Kiran ya biyo bayan matakin da jami’in yaɗa labaran ya ɗauka na zaɓar wasu ‘yan Jarida a matsayin wadanda za su yi rahoto a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da ke gudana a Kaduna da yin watsi da wasu ‘yan Jaridar. Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Yi Wa Matawalle Tawaye

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya daga jihar su Shida waɗanda suka koma jam’iyyar APC tare da gwamna Matawalle sun yi amai sun lashe. ‘Yan majalisar wakilan sun sake komawa jam’iyyar PDP kuma sun karɓi tikitin takara a babban zaɓen 2023 ba tare da hamayya ba. ‘Yan majalisar sun sake komawa PDP ne sakamakon yarjejeniyar da aka yi yayin sulhun gwamna Bello Matawalle na Zamfara, tsohon gwamna Abdul-Aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa. Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Isa Ashiru Ya Lashe Zaben Fidda Gwani A PDP

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Maƙarfi da Kudan a majalisar wakilai Alhaji Isa Ashiru Kudan ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP da babban rinjaye. Alkaluman sakamakon zaɓen sun nuna cewar Isa Ashiru Kudan ya samu kuri’u mafiya rinjaye inda ya doke abokan takarar shi da samun kuri’u 414. Tuni wasu daga cikin abokanan takarar tashi suka amince da kayen har suka miƙa sakon taya shi murna bisa ga nasarar da ya samu. Tuni tsohon Sanata…

Cigaba Da Karantawa

Kisan Harira: Tsagerun Inyamurai Za Su Dandana Kudarsu – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan da ’yan haramtacciyar kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB suka yi wata ’yar Arewa mai suna Harira da ’ya’yanta su hudu a Jihar Anambra. Shugaban ya bayyana kisan nata da ma na sauran mutane da kungiyar ke ci gaba da yi a yankin a matsayin dabbanci, inda ya ce za su ɗanɗana kuɗarsu. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shi, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Laraba, Buhari ya gargaɗesu cewa su jira tsattsauran mataki daga jami’an tsaro.…

Cigaba Da Karantawa

Harin Jirgin Abuja: Iyalan Fasinjoji Sun Shiga Rudani

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Iyalan fasinjojin jirgin kasan da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su bayan harin da suka kai musu akan hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun roki shugaban ƙasa Buhari da ya ceci iyalai, ‘yan uwa da abokan nasu, ta hanyar gaggauta amsa bukatar maharan. Iyalan fasinjojin sun bayyana haka ne, yayin zanga-zangar lumanar da suka yi da safiyar Larabar nan, a cigaba da kokarin jan hankalin gwamnatin tarayya domin ceto ‘yan uwan nasu. Masu zanga-zangar sun bayyana damuwa kan barazanar da…

Cigaba Da Karantawa

Kayyade Kudaden Kananan Hukumomi: Gwamnoni Za Su Garzaya Kotu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar gwamnoni ta ce za ta ɗaukaka ƙara game da hukuncin wata babbar kotu da ya kori ƙarar da suka shiga suna ƙalubalantar matakin da sashen tattara bayanan sirri kan hada-hadar kuɗi na ƙayyade kuɗaɗen da ƙananan hukumomi za su rika kashewa a kullum. A hukuncin da babbar kotun ta yanke ta ce gwamnonin ba su da hurumin hana kayyade naira dubu 500,000 a matsayin kuɗaɗen da ƙananan hukumomi za su rika kashewa a kullum ba. Abdulrazak Bello Barkindo…

Cigaba Da Karantawa