Da Dumi-Dumi: An Daga Darajar Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Yola Zuwa Asibitin Jami’a

Bayan tsawon lokaci da aka dauka ana jira daga ƙarshe shugaban kasa muhammadu Buhari ya amince da cibiyar kiwon lafiya ta tarayya dake Yola wato FMC Yola da ta zama asibitn koyarwa na Jami ar Modibbo Adama dake Yola. Darakta yada labarai na ofishin Sakataren gwamnatin tarayya Mr Willie Bassey ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja. Amincewar dai ta biyo bayan bukatar al’umma jihar ta Adamawa tare da gwamnatin jihar wanda hakan zai taimaka wajen horas da Likitoci har ma da inganta kiwon lafiya…

Cigaba Da Karantawa

Gombe: An Tsaurara Tsaro Bayan Kisan Deborah A Sokoto

Labarin dake shigo mana daga Jihar Gombe na bayyana cewar biyo bayan kisan da akayi wa wata ɗaliba mai suna Deborah a kwalejin ilimi na Shehu Shagari a jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad SAW. Rundunar ‘yan Sanda a Gombe ta gudanar da tattaki inda jami’an rundunar a cikin Motoci dauke da manyan makamai suka rinƙa zagaye cikin anguwannin da Majami’u don tabbatar da cewa abubuwa na tafiya lafiya. Da yake ƙarin haske akan tattakin kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Gombe ASP Mu’azu Abubakar yace an yi tattakin…

Cigaba Da Karantawa

Taraba: Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APC

BASHIR ADAMU, JALINGO Wani sabon rikici ya barke a Jam’iyyar APC Jihar Taraba sakamakon sauya zababbun Shugabannin Kananan Hukumomi guda hudu. A ranar Asabar ne Jam’iyyar APC ta sake rantsar da wasu sabbin Shuwagabanni Kananan Hukumomin Ussa, Wukari, Ibi da Takum. Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Taraba, Ibrahim Tukur El-sudi ne ya jagoranci rantsarwan, inda wasu bayanai ke cewa yayi hakan ne bisa umurnin Uwar Jam’iyyar ta Kasa da ta turo mishi da sunayen wadannan sabbin Shugabanni hudu. Inda yace wadannan zababbun Shugabannin da aka sauya, su daina bayyana kansu…

Cigaba Da Karantawa

Zamba Cikin Aminci: EFCC Ta Damke Tsohuwar Shugabar Majalisa

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa EFCC, ta kama tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan ƙasar, Ms Patricia Etteh. An ruwaito cewa EFCC ta yi awon-gaba da Ms Etteh ne kan zargin almundahanar kuɗaɗe a ma’aikatar raya yankin Neja Delta wato NDDC da yawansu ya kai naira miliyan 287. Wata majiyar EFCC ta fada wa jaridar Punch cewa Ms Etteh ta karbi naira miliyan 130 daga kamfanin Phil Jin Project Limited da NDDC ta bai wa kwangilar naira miliyan 240 a 2011. A kan haka a yanzu…

Cigaba Da Karantawa

2023: Zan Dawo Da Najeriya Hayyacin Ta – Atiku

Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya bada tabbacin dawo da Najeriya cikin hayyacin ta idan ya yi nasarar zama shugaban ƙasa a shekarar 2023. Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a sakatariyar jam’iyar PDP ta jihar Kaduna a ziyarar da ya kawo jihar domin neman goyon bayan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. “APC ta lalata Najeriya fiye da yadda ake zato, gyaruwar ƙasar ya ta’allaka da samun jajirtaccen Mutum kamar ni, ina da tabbacin samun nasara idan aka tsayar dani takara”. Tun farko…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Tarin Matafiya A Hanyar Abuja

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ‘yan Bindiga masu garkuwa da mutane sun sace mutane da dama a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata. Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Katari da misalin 4:30 na yammaci. Ya bayyana cewa akwai motoci da dama waɗanda suna ajiye a kan ɓangaren zuwa Kaduna da ɓangaren dawowa da aka yi awon gaba da masu motocin. Ya kuma ce bayan faruwar lamarin jami’an tsaro masu ɗumbin yawa…

Cigaba Da Karantawa

Badakalar Miliyan 20: Jama’atu Ta Maka Sarkin Zazzau Kotu

Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam reshen Zariya jihar Kaduna ta maka Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli a kotu bisa zarginsa da karkatar da kuɗi naira miliyan 20 da ma’aikatar sufuri ta tarayya ta ba ta. JNI ta ce an biya cekin kuɗin ne ga kungiyar a matsayin diyyar karɓe filinta na Kwalejin Larabci domin aikin hanyar jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Zariya. A karar da aka shigar a 25 ga Afrilu a babbar kotun jihar Kaduna, shugaban ƙungiyar da sakatare Zaharadeen Maccido da Usman Maccido, sun bukaci a saki cakin ɗin. Masu…

Cigaba Da Karantawa

2023: APC Ta Musanta Sauya Jadawalin Shirye Shiryen Zabe

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC ta musanta cewa ta sauya jadawalin shirye-shiryen zaɓen 2023 Jam’iyyar APC ta buƙaci jama’a da su yi watsi da raɗe-raɗin da ake ta yaɗa wa cewa ta sauya jadawalinta shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2023. Felix Morka, Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar, a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Litinin, ya ce rahoton sauya zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyar na bogi ne, ya kamata a yi watsi da shi. “An ja hankalinmu kan wani labari…

Cigaba Da Karantawa