Zagin Annabi: Ba Mu Yarda Wani Ya Yi Zanga-Zanga A Kaduna Ba – El Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya haramta gudanar da “zanga-zangar addini” game da batun ɓatanci da aka yi wa Annabi Muhammadu (SAW) a Jihar Sokoto. Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Kaduna ta fitar a yau Asabar ta ce an ɗauki matakin “saboda yuƙurin wasu marasa kishin ƙasa” na shirya zanga-zangar adawa da kuma goyon bayan lamarin. “An faɗa wa Gwamna El-Rufai halin da ake ciki kuma ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da hana duk wani nau’i na zanga-zangar addini a jihar,” a cewar sanarwar da Kwamashinan…

Cigaba Da Karantawa

‘Ya’yan Sarkin Kano Na Neman Rayuwata – Tsohuwar Jarumar Kannywood

Tsohuwar jarumar Kannywood, wadda aka fi sani da sunan Maijidda Ibrahim, na neman agajin ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam da sauran jama’a kan halin ha’ula’in da ta ke ciki Lokacin da ta ke fitacciyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, sunan ta Maijidda Ibrahim, yanzu kuma Hajiya Hauwa Bello Ado Bayero. Ta na ɗaya daga cikin ɗimbin mata ‘yan fim da su ka yi aure kuma su na zaune a gidan miji. Tsawon shekaru 21 kenan tun da tsohuwar jarumar, wadda aka fi sani da sunan Maijidda Khusufi saboda wani fitaccen…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Kara Yawan Adadin Daliban Da Muke Ciyarwa – Ministar Jin Kai

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Yobe na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta bada umurnin sanya suna sabbin dalibai milyan biyar cikin wadanda ake baiwa abinci kullum a makarantun gwamnati a fadin tarayya. Ministar tallafi, walwala da jin dadin jama’a, Hajia Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan a Damaturu, jihar Yobe, yayin taron raba kayan girki ga ma’aikatan jihar. Ministar, wacce ta samu wakilcin mataimakin daraktan Braille Library Bauchi, Hassan Maidugu, ya ce an yi wannan shiri ne don kawar da talauci da inganta rayukan al’umma. Ya kara da cewa kawo yanzu…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: An Damke Kansilan Dake Harka Da ‘Yan Bindiga

Dubun wani Kansila mai suna Abdulraman Adamu dake wakiltar Yankin Kibiya a karamar hukumar Soba ya faɗa hannun ƴan sanda bayan sun kamashi yana safarar bindiga AK 47 ga ƴan bindigan dake tabargaza a yankin Giwa. Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya bayyana cewa jami’ai sun damke Adamu ne da dare wajen ƙarfe 8 na dare a bisa babur ɗauke da bindigar da harsasai zai a yankin karamar hukumar Giwa. Bayan an tuhume sa sai aka gano zai kaiwa wasu ƴan bindiga ne da yake wa aiki a…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Yi Tir Da Kisan Deborah A Sokoto

Shugaban Kasa Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyayen ɗalibar kwalejin Shehu Shagari dake Sokoto wanda ajali ya iske ta bayan an zarge ta da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW. Buhari ya ce doka ba ta ba wani damar yanke hukunci kai tsaye ba. komai na da hurumin sa. Idan an yi laifi sai kuma a bari waɗanda hukunci ke hannunsu su yanke shi ba kowa ya yi gaban kansa ba. A sakon da ya fitar wanda kakakin shugaban ya saka wa hannu Garba Shehu, Buhari ya yabawa wa gaggawar…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Za Ta Taimaki Sudan Ta Kudu A Yaki Da ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin taimaka wa ƙasar Sudan ta Kudu a yaƙi da ‘yan bindiga da kuma haɗin kan ƙasar. Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake karɓar baƙuncin wakilin Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. “Za mu duba halin da kuke ciki don ganin yadda za mu taimaka,” inji Buhari cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar. Wakilin na musamman ya yi…

Cigaba Da Karantawa