Ba Za A Binciki Wadanda Suka Sayi Fom Miliyan 100 Ba – Fadar Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaban kasar ba zai binciki yadda yan takara suka samu kudaden da suka kashe wajen siyan fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba. Mallam Garba Shehu ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin Channels TV a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu. Shehu ya bayyana cewa aikin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da kungiyoyin jama’a ne gano yadda aka…

Cigaba Da Karantawa

2023: Bamu Da Zabin Da Ya Wuce Tinubu – El Rufa’i

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamna Nasir El-Rufai ya fito fili ya bayyana goyon bayan sa ga kudirin jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na takarar shugabancin kasa a 2023. El-Rufai ya bayyana hakan ne a dandalin Murtala da ke Kaduna inda Tinubu da tawagarsa da suka haɗa da tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, da tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribado da sauran manyan baki suka kai wa wakilai APC na jihar ziyarar neman goyon baya. Gwamna El-Rufai ya ce zai…

Cigaba Da Karantawa

Masu Adawa Da Takarata Za Su Mutu Da Bakin Ciki – Gwamnan Babban Banki

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan babban bankin ƙasa (CBN) Godwin Emefiele ya ce yana jin dadin duk wani wasan kwaikwayon da ke zagaye da burinsa na takara a 2023, kuma yana da tabbacin masu adawa dashi za su kunyata. Emefiele ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, ranar Alhamis. Da aka tambaye shi game da martaninsa…

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aikin ASUU: Buhari Ya Ba Dalibai Hakuri

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga daliban jami’o’in kasar da su kara hakuri, yana mai cewa gwamnati na iya bakin kokarinta don ganin an kawo karshen yajin aikin da malamai ke yi. Tun a watan Fabrairu kungiyar malaman jami’o’in ta ASUU ta shiga yajin aiki, a kuma farkon makon nan ta kara tsawaita shi har zuwa watan Agustan bana. Kungiyar na zargin gwamnati da abin da ta kira “rashin kulawa” da gwamnati ke nunawa wajen neman maslaha kan batun. Sai…

Cigaba Da Karantawa