SHUGABANCIN NIJERIYA 2023: TAKARAR GWAMNA BADARU A JAMA’IYAR APC
………………..
Ahmed Ilallah

Ta tabbata a wannan karon ma Gwamnan Jigawa mai barin gado zai yi takarar shugabancin kasar Nijeriya, amma fa akasarin takarkarin da wayanda ya gada suka yi a baya tamkar taka-kara ne, kusan cewar babu wani tasiri da takarar tayi, face a kira su da sun taba takara. Shin wannan takarar ma ta gwamna Badaru zata zamanto takara ko kuma tayi tasirin da dole sai an dama dashi a fagen siysar kasar nan? Ko kuma ita ma zata zamanto taka-kara? A siyasar bana, Jama’iyar APC mai mulki tazo da wani…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: ‘Yan Takarar APC Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi

Rahotannin dake shigo mana daga Yola babban birnin jihar Adamawa na bayyana cewar ‘Yan takarar shuagabanin kananan hukumomi da Kansilolinsu na Jam’iyar APC sun yi Allah wadai da sakamakon zaɓen kananan hukumomi da aka gudanar kwananan a jihar. Honorabul Ahmed Rufa’i ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatarwa manema labarai jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Yola. Ahmed Rufa’i yace lamarin baiyi dadi ba ko kadan kasancewar sun shiga saƙo-saƙo domin neman kuri’a amma ace wai basu da kuri’ar da zai basu damar cin zabe.…

Cigaba Da Karantawa

Taraba: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Sojoji

Rahotanni daga Jalingo babban birnin jihar Taraba na bayyana cewar Yan bindiga sun kashe sojoji shida yayin da suke hanyar su ta zuwa wurin da aka kai hari a Tati, wani ƙauye da ke karamar hukumar Takum, a cewar rundunar Sojojin Najeriya cikin wani sako na cikin gida da ta fitar. A cewar takardar da rundunar sojojin ta bataliya 93 da ke Takum ta aike, kawo yanzu ba a gano inda kwamandan bataliyar, E.S. Okore, mai muƙamin laftanar kanal ya ke ba. Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 10 na…

Cigaba Da Karantawa

Kano: NNPP Na Yi Wa APC Yankan Kauna

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar jam’iyyar NNPP ta sake yin kamu a jihar inda ta samu karin mabiya a makon nan. Jam’iyyar hamayyar ta NNPP ta samu karin ‘yan majalisar dokoki uku da suka sauya-sheka daga APC kamar yadda suka sanar a wasikar da suka fitar. A mabanbantan takardu da suka aikawa shugaban majalisar Kano a ranar 5 ga watan Mayun 2022, sun sanar da ficewa daga APC da kuma komawarsu sabuwar jam’iyyar NNPP. Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na majalisar dokokin jihar…

Cigaba Da Karantawa

2023: Ina Da Tabbacin Nasarar Tinubu – Tsohon Sakataren Gwamnati

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana yaƙinin da yake dashi na samun nasarar Tinubu a babban zaben dake tafe na shekarar 2023: Babachir ya bayyana haka ne a Abuja, a ranar Laraba, 11 ga watan Afrilu, jim kadan bayan wata kungiyar goyon bayan Tinubu ta mika fom din takarar shugaban kasa na Tinubu a sakatariyar jam’iyar APC na Kasa. Tawagar magoya bayan Tinubu karkashin jagorancin gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da…

Cigaba Da Karantawa

APC Ta Tsawaita Wa’adin Zabukan Fidda Gwani

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyya mai mulki, APC ta ƙara wa’adin ranakun zaɓukan fidda-gwanin takarar gwamnoni, sanatoci, wakilan tarayya da na jihohi. Sakataren Tsare-tsaren Jam’iyyar Suleiman Argungu ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja. Da fari an shirya za a yi zafin fidda-gwanin gwamnoni a ranar 18 Ga Mayu, shi kuma na Majalisar Jihohi a ranar 20 Ga Mayu, za a yi na Majalisar Tarayya a ranar 22 Ga Mayu, na Sanatoci kuwa a ranar 24 Ga…

Cigaba Da Karantawa

2023: Duk Wanda Zai Yi Takara Ya Aje Aiki – Buhari Ga Ministoci

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci ministocinsa masu son takara su yi murabus daga nan zuwa 16 ga watan Mayu. Ministan yaɗa labarai Lai Mohammed ne ya sanar wa da manema labarai hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa na mako-mako a ranar Laraba da aka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Tun da fari a ranar 25 ga watan Fabrairun 2022 Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan majalisa tarayyar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84…

Cigaba Da Karantawa