Bauchi: An Damke Wadanda Suka Kashe ‘Yar Shekara 5 Da Cusa Gawarta A Buhu

Daga Adamu Shehu Bauchi Rundunar Jami’an Tsaro da akafi sani da suna (Civil Defence) sun samu nasarar cafke mutum biyu wadanda ake zargin sun sace wata yarinya mai suna Kadijah Abdullahi ‘yar shekara biyar suka kashe ta suka cusa ta a buhu suka rufe a wani kangon kicin dake wani gida a unguwan kauyen na Rabi dake a karamar hukumar Toro Jihar Bauchi. Shugaban rundunar na jihar Nurudden Abdullahi da yake zantawa da manema labarai a Shalkwatar rundunar dake Bauchi, yace bayan samun labarin ta’asar Jami’an tsaro suka shiga aikinsu…

Cigaba Da Karantawa

Pantami Zai Jagoranci Taron Kungiyar Sadarwa Ta Duniya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Sadarwa, Isa Pantami zai jagoranci taron Kungiyar Bayanai ta Duniya ta shekarar 2022 bisa nadin da Kungiyar Sadarwa ta Kasa da kasa (WSIS) ta 2022 ta yi masa. Za a yi taron ne a hedkwatar Kungiyar Sadarwar ta Kasa da Kasa da ke Geneva babban birnin kasar Switzerland. Kamar yadda takardar da hadimin ministan na bangaren bincike da ci gaba, Dr Femi Aduluyi ya saki ta nuna, an sanar da ministan batun nadin na shi ne ta wata…

Cigaba Da Karantawa

Pantami Zai Jagoranci Taron Jungiyar Sadarwa Ta Duniya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Sadarwa, Isa Pantami zai jagoranci taron Kungiyar Bayanai ta Duniya ta shekarar 2022 bisa nadin da Kungiyar Sadarwa ta Kasa da kasa (WSIS) ta 2022 ta yi masa. Za a yi taron ne a hedkwatar Kungiyar Sadarwar ta Kasa da Kasa da ke Geneva cikin kasar Switzerland. Kamar yadda takardar da hadimin ministan na bangaren bincike da ci gaba, Dr Femi Aduluyi ya saki ta nuna, an sanar da ministan batun nadin na shi ne ta wata takarda…

Cigaba Da Karantawa

Komawar Jonathan APC Babban Abin Mamaki Ne – Gwamnan Ebonyi

Gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi, ya ce idan har tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya koma jam’iyyar APC, labarin zai zama babban abin mamaki da zai shiga littafin tarihin duniya. A ranar Litinin, hadakar kungiyoyin arewa su ka siya wa tsohon shugaban kasar fom din takara karkashin jam’iyyar APC, inda su ka bukaci ya tsaya takara a shekarar zaɓe ta 2023. Yayin da Umahi ya ke jawabi a gidan gwamnatin jihar ranar Talata, Ya ce an sayi fom din ne musamman don a tozarta Jonathan a babbar shekarar zaɓe ta…

Cigaba Da Karantawa

2023: Ya Kamata Buhari Ya Samu Karin Wa’adi Na Uku – Babban Lauya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babban Lauya Robert Clarke (SAN), ya yi kira da a kara wa Shugaba Buhari wa’adin mulki bayan kammala mulkinsa na biyu a 2023. Babban lauyan, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin ya bayyana cewa watannin da ke gabanin zaben 2023 ba su isa su kawo karshen rashin tsaro ba, balle a iya zabe cikin kwanciyar hankali. Da yake magana a gidan talabijin na Arise, Clarke ya ƙara da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa shugaban kasa…

Cigaba Da Karantawa