Tsaro: An Yi Wa Arewa Kofar Raggo – Zakzaky

A sakon da ya fitar na murnar bikin sallah karama, Shugaban Ƙungiyar IMN (Shi’a) ta ƙasa Sheikh Ibrahim Yakubu El Zakzaky ya bayyana yadda maƙiya suka taso yankin Arewa gaba. Shugaban kungiyar ta ‘yan Shi’a ya zayyano wasu abubuwa guda uku waɗanda sune jigajigan karfin arzikin Arewa kuma ake burin ruguza su. 1-Noma. wadda ita ce tushen arzikin mutanen yankin, yanzu ta gagara, an hana manoma aiki an kore su daga garuruwan su, wanda ya zauna za a kashe shi. 2-Kiwo. Makiyaya an kashe ana kwashe dabbobin su. 3-Kasuwanci. Sufurin…

Cigaba Da Karantawa

Shugabancin Kasa: Kungiyar Fulani Ta Saya Wa Jonathan Fom

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da babban zaben shekarar 2023 ke cigaba da karatowa, wata kungiya karkashin ‘kungiyar fulani’ ta saya wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan fom din takarar shugaban kasa kan tsabar kudi naira miliyan N100. Hotunan da TVC News ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna wasu cikin shugabannin kungiyar dauke da fom ɗin na takarar shugabancin ƙasa a Jam’iyya mai mulki ta APC. Idan za a iya tunawa a watan Afrilu 2022, wasu mutane sun yi tattaki…

Cigaba Da Karantawa