Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Fice Daga Abuja Zuwa Abidjan

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na kan hanyar zuwa Abidjan babban birnin Ivory Coast domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan kare kare muhalli musamman yadda za a magance kwararowar hamada. Sanarwar da fadar shugaban ta fitar ta ce Buhari zai bar Abuja a ranar Lahadi zuwa Abidjan, domin halartar taron na kwana biyu da za a soma a ranar Litinin. Taron ya shafi yadda za a magance kwararowar hamada da fari da zabtarwar ƙasa da sauran matsalolin muhalli, zai…

Cigaba Da Karantawa

Gombe: An Yi Tir Da Sake Bayyanar ‘Yan Kalare

Al-ummar jihar Gombe na cigaba da yin Allah wadai da tofin Allah ya tsine akan sake bullowar aika-aikan matasa ‘yan bangar siyasa da akafi Sani da ‘yan kalare a jihar. Idan dai za a iya tunawa kwanan nan ‘yan kalare a Gombe sun sake dawo da mummunar aika-aikan su na fadace_fadace dake kai wa ga asarar rayuka da dukiyoyi, don ko a kwanan nan ‘yan kalare sun kashe mutum uku a unguwar Jeka da fari baya ga wani jami’in soja da suka kashe a unguwar Dawaki duk a cikin garin…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Bambancin Kudan Kan Sauran ‘Yan Takara

A fili yake da akwai gagarumin banbanci a tsakanin mai girma Alhaji Isa Ashiru Kudan da sauran ‘yan takara dake hanƙoron hawa Kujerar gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2023. Idan ana magana ta fuskar gogewa da cancanta Isa Ashiru Kudan ya sha gaban dukkanin sauran ‘yan takara walau waɗanda suka fito a Jam’iyya guda da su ta PDP ko kuma waɗanda suke a sauran jam’iyyu. Masana ilimin siyasar duniya sun yi ittifaki akan cewa shugaba nagari dole zai kasance wanda ya cika wasu sharudda a rayuwarsa waɗanda suka haɗa ilimi…

Cigaba Da Karantawa

Sarkin Yakin Zaben Tinubu Ya Fice Daga APC

Tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmuminu Jibril Kofa, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar APC. Kofa, wanda shine kuma Daraktan Yaƙin Zaɓen Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook a yau Asabar. A takaitaccen sakon da ya wallafa, Kofa ya ce ya yi iyaka baƙin ƙoƙarinsa a kan jam’iyyar APC, saboda haka lokaci yayi da zaiyi gaba a siyasar sa. ya kuma ƙara da cewa cikin awanni 24 zai sanar da makomar sa a siyasa. “Nayi wa APC…

Cigaba Da Karantawa

Za A Kara Farashin Kudin Kiran Waya A Najeriya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta ƙasa ta ce ta samu takarda daga ƙungiyar kamfanonin sadarwa na ƙasar na neman yin ƙarin kuɗin kiran waya da kuma data sakamakon tsadar gudanar da ayyukansu. Rahotanni sun ce takardar da ƙungiyar ta gabatar na neman yin ƙarin kashi 40 cikin 100 na farashin kiran waya da aika saƙo. Kamfanonin na son yin ƙarin ne na kira daga N6.4 zuwa N8.95, farashin aika saƙo kuma zai koma N5.61 maimakon N4. Hauhawan farashi a…

Cigaba Da Karantawa

Shugabancin Kasa: Har Yanzu Ban Sayi Fom Ba – Gwamnan Babban Banki

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya ce bai yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba tukunna a babban zaɓen 2023. Mista Emefiele mai shekara 60 na mayar da martani ne bayan rahotannin da suka karaɗe kafofin yaɗa labarai a ciki da wajen ƙasa cewa ya sayi fom ɗin takarar ranar Juma’a. “Ina godiya da sha’awar da wasu ƙungiyoyi ke nunawa gare ni don na fito takarar shugaban ƙasa,” in ji shi. “Sai dai idan na yanke hukuncin…

Cigaba Da Karantawa

An Roki Kamfanonin Jiragen Sama Su Janye Aniyar Dakatar Da Aiki

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin ta roƙi kamfanonin jiragen sama da kada su dakatar da aiki kamar yadda suka yi barazana daga Litinin ɗin nan. An ruwaito wata sanarwa daga ofishin Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika na cewa hakan zai yi tasiri kan tattalin arziƙin ƙasa “wanda da ma yake a ƙuntace”. Ministan ya bayyana damuwarsa kan “wahalhalun da kamfanonin ke fuskanta wajen samun man jirgin” amma ya ce ma’aikatarsa ba za ta iya yin wani abu ba. “Abin damuwar shi ne samar da man…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Binciki Inda ‘Yan Siyasa Suka Samu Kudin Takara – EFCC

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce tana sa ido kan tushen kuɗaɗen da ake amfani da su wajen sayen fom ɗin takara na jam’iyyun siyasa. Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ne ya bayyana haka a wata hira da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi a ranar Juma’a. Ya ce hukumarsa ta EFCC na haɗa kai tare da hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC domin gano inda aka samo kuɗaɗen da ƴan siyasa ke…

Cigaba Da Karantawa