Komai Zai Daidaita A Najeriya – Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya baiyana ƙwarin gwiwa cewa duk da ɗumbin matsalolin da ke damun Nijeriya, komai zai zama tarihi. Obasanjo ya baiyana hakan ne a wani taron addini na ƴan ɗariƙar Deeper Life a birnin Abeokuta a ranar Talata, wanda ya halarta ta yanar gizo. Obasanjo ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su koma ga Allah domin samun sauƙin matsalolin da su ke damun ƙasar. A cewar Obasanjo, duba da irin matsalolin da Nijeriya, Afirka da ma su iya ke ciki, babu abinda mu ke buƙatar…

Cigaba Da Karantawa

Karya Ne Ban Raba Motoci Ba – Malami

Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Ƙasa, Abubakar Malami ya musanta labaran da su ka yaɗu a jiya na cewa ya raba motoci na-gani-na-faɗa ga magoya bayan sa. Malami ya ƙaryata labarin ne a yayin wata ganawa da manema labarai jiya Talata a Birnin Kebbi. A cewar sa” a kwanakin nan ina shan sharri iri-iri, ta sama, ta ƙasa ta tsakiya, wasu a nan cikin gida wasu kuma daga ƙasashen waje. Har da sahrrin cewa wai na raba motoci ga masu tsada ga ƴan jam’iyar APC. “A matsayina na mutum mai…

Cigaba Da Karantawa

Shugabancin Kasa: Shugaban Majalisa Ya Bayyana Aniyarsa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan zai fito takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iya mai mulki ta APC. Lamarin yunƙurin fitowar Lawan alama ce ta fitowar wata ‘tauraruwa mai wutsiya’ a cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa a APC. Fitowar takarar Lawan zai kasance shi ne ɗan takara na biyu daga Arewa, bayan Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi. Zai ƙalubalanci ‘yan Kudu irin su Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi da sauran su da dama. Idan ba a manta…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Na Bukatar Megawat Dubu 100 Na Magance Matsalar Lantarki – Minista

Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Farfesa Barth Nnaji, ya bayyana cewa Nijeriya na buƙatar megawat dubu 100 na wuta in har ta na buƙatar magance matsalar wutar lantarki a ƙasar. Nnaji ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a kan makomar wutar lantarki a ƙasa ranar Juma’a a Enugu. Ya ce ƙasar na fama da matsaloli wajen samar wa, yaɗa wa da rarraba wutar lantarki a ƙasa. Ya ce duk wannan shi ne ya sanya zai yi wuya a samu isashshiyar wutar lantarki ga ƴan kasa.

Cigaba Da Karantawa

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Ziyarar Aiki A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana bayan saukar Sakataren Majalisar Guterres ya ziyarci birnin Maiduguri na jihar Borno da har yanzu ke fama da matsalar hare-haren mayakan Boko Haram da na ISWAP da suka balle daga kungiyar. Yayin ziyarar tasa a Borno, sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya gana da gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum a birnin Maiduguri, daga bisani kuma ya gana da wasu daga cikin iyalan da rikicin Boko Haram ya shafa tsawon fiye da shekaru 10. Daga jihar ta Borno, Antonio Guterres ya…

Cigaba Da Karantawa