Kaduna: Majalisa Ta Tantance Umma Aboki Matsayin Kwamishinar Kasafi

Rahotannin dake shigo mana daga zauren Majalisar dokokin Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan majalisar Dokokin jihar sun tantance Hajiya Umma Yusuf Aboki, a matsayin kwamishiniyar kasafi da tsare tsare yau Talata. Hajiya Umma, ta gaji tsohon kwamishinan ma’aikatar Muhammad Sani Dattijo, wanda ya ajiye muƙamin nasa don yin takarar Gwamnan jihar ƙarkashin inuwar jam’iyyar APC a zabukan 2023 dake tafe.

Cigaba Da Karantawa

2023: Ba Na Tare Da Osinbajo A Takarar Shugabancin Kasa – Tinubu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ba ɗan sa bane ba a siyansace kuma ba ya tare dashi a takarar shugabancin kasa ta 2023. Tinubu ya yi wannan furucin ne a Abuja yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da gwamnonin APC 12 kan batun takararshi da ya yi. Taron wanda ya gudana a gidan gwamnan Kebbi dake Asokoro, a birnin Abuja, ya zo ne awanni bayan mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa…

Cigaba Da Karantawa

An Haramta Wasan Tashe A Kano

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta haramta “Tashe”, wani wasan barkwanci da ake yi duk shekara bayan kwanaki goma na farkon watan Ramadana. Kakakin rundunar, SP Abdullaji Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a wata takarda da rundunar ta fitar ranar Litinin kuma aka rarraba ga manema labarai a Kano. Kamar yadda takardar ta bayyana, dalilin da yasa aka haramta al’adar mai cike da tarihi shine yadda hatsabibai ke amfani da damar wajen cutar da al’umma da sauran abubuwa marasa…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: Ina Burin Sake Dawowa Gwamna – Bindow

Rahotanni daga Yola babban birnin jihar Adamawa na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Umar Jibrilla Bindow, ya bayyana burinsa na neman wani wa’adi a matsayin gwamna a karkashin APC a 2023. An ruwaito Umar Jibrilla Bindow yana cewa zai so a ba shi wata damar domin ya karasa ragowar shekaru hudu da suka rage masa a gidan gwamnati. Da yake zantawa da manema labarai a garin Yola, jihar Adamawa a ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu 2022, Jibrilla Bindow ya nemi goyon bayan al’ummar Jihar da su sake bashi damar.…

Cigaba Da Karantawa

Muna Kashe Biliyan 10 Duk Wata Wajen Ciyar Da Dalibai – Minista

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya na kashe kimanin naira bilyan 10 a wata wajen shirin ciyar da daliban makarantun firamare a fadin tarayya. Wannan aiki na gudana ne karkashin Ministar tallafi, jin kai, da jin dadin jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq. Jagoran shirin, Dr Umar Bindir, ya bayyana hakan ranar Litinin, a taron masu ruwa da tsaki na kwana biyu kan samar da takardar doka kan shirin kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito. Dr Bindir ya bayyana cewa akwai muhimmancin…

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ganawar Musamman Da ASUU

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta hannu Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige, sun yi ganawa da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU, a ranar Litinin. Kwanaki 56 kenan da ASUU ta shiga yajin aiki sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar. ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanyar karshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin…

Cigaba Da Karantawa