Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan YaÉ—a Labarai a Najeriya Lai Mohammed ya tabbatar da kai hari kan sansanin sojan Ć™asar da ‘yan bindiga suka kai a Jihar Kaduna. Ministan ya ce duk da cewa kafofin yaÉ—a labarai da dama sun ruwaito harin amma sun gaza wajen ruwaito yadda sojojin Najeriya suka fatattaki maharan. Sojoji aĆ™alla 11 rahotanni suka ruwaito an kashe a harin na ranar Lahadi lokacin da maharan suka far wa sansanin nasu da ke yankin Birnin Gwari. Kazalika, an Ć™ona motocin soja masu sulke…
Cigaba Da KarantawaDay: April 7, 2022
Mika Matatun Mai Ga Tompolo: Matasan Arewa Sun Gargadi NNPC
Kungiyar haÉ—in kan matasan Arewa ta yi tir gami da Allah wadai da yunkurin Kamfanin NNPC karkashin jagorancin Mele Kyari na miĆ™a kula da Matatun man fetur ga kasurgumin dan ta’adda Oweizide Ekpemupolo wanda aka fi sani da suna Tompolo. Matasan na Arewa sun yi wannan gargadi ne a wani taron manema labarai da suka kira wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna. Da ya ke jawabi a yayin taron mataimakin Kakakin Ć™ungiya na kasa Abdulsalam Mohammed Kazeem, yace kiran nasu ya zama wajibi duba da irin…
Cigaba Da KarantawaDa Dumi-Dumi: Jonathan Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yammacin ranar Laraba ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi hatsarin mota a Abuja wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mukarrabansa biyu nan take. ĆŠaya daga cikin masu taimaka masa, wanda ya tabbatar da afkuwar hatsarin, ya ce Jonathan na cikin koshin lafiya a halin yanzu. Hadarin ya afku ne a lokacin da tsohon shugaban kasan ke kan hanyar sa daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe zuwa gidansa da ke Abuja. A cewar majiyoyi daga makusanta Jonathan,…
Cigaba Da KarantawaBa Kudi Muke Bukata Ba – ‘Yan Fashin Jirgin Abuja
A karon farko, ‘yan bindigar da suka kai hari kan jirgin Ć™asan fasinja da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna sun yi jawabi, inda suka yi barazanar kashe fasinjojin da suka sace matuĆ™ar gwamnati ba ta biya musu buĆ™atunsu ba. A jiya ne, wani bidiyo da ya bayyana, ya nuna wasu daga cikin maharan É—auke da bindigogi suna iĆ™irarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin Ć™asan a ranar Litinin din makon jiya. Bidiyon, wanda bai kai tsawon minti 1:30 ba, ya nuna huÉ—u cikin ‘yan bindigar sanye da kakin…
Cigaba Da KarantawaHarin Jirgin Abuja: An Sako Shugaban Bankin Manoma
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ćłan bindiga da suka kai harin bam a jirgin Ć™asa a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun saki shugaban bankin manoma Alwan Ali Hassan É—aya daga cikin fasinjojin da suka yi awon gaba da su a cikin jirgin. An sake shi ne a ranar Laraba, kamar yadda wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar wa BBC. A ranar Litinin 28 ga watan Maris Ć´an bindiga suka kai harin bam a jirgin Ć™asa da ke kanyar zuwa Kaduna daga Abuja. Hukumar kula…
Cigaba Da KarantawaDa Dumi-Dumi: Najeriya Ta Janye Dokar Korona
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta cire dokar hana fita ta tsakar dare da kuma taruwar jama’a a tarukan bikin aure da na waĆ™e-waĆ™e waÉ—anda aka saka da zimmar yaĆ™i da annobar korona. Kwamatin yaĆ™i da cutar na shugaban Ć™asa ya ce an É—auki matakin ne sakamakon raguwar mutanen da ke kamwua da cutar a Ć™asar. Najeriya ta saka dokokin ne tun bayan É“ullar annobar cikin Ć™asar a watan Fabarairun 2020. Wata sanarwa daga kwamatin ta ce an kuma samu raguwar haÉ—arin…
Cigaba Da Karantawa2023: APC Za Ta Fitar Da Dan Takarar Shugabancin Kasa A Watan Mayu
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki za ta gudanar da zaÉ“ukan fitar da ‘yan takara a muĆ™amai daban-daban a watan Mayun 2022. Rahotanni sun bayyana cewar jam’iyyar za ta fitar da É—an takarar shugaban Ć™asa ranar 30 ga watan Mayu. Za a fara zaÉ“uakan ne da na ‘yan majalisar jiha a ranar 17 ga Mayu, yayin da da na ‘yan majalisar wakilai zai biyo baya ranar 19, sai kuma na ‘yan majalisar dattawa ya gudana a ranar 21. ZaÉ“en fitar da…
Cigaba Da Karantawa