Sukar Gwamnati: An Dakatar Da Sheikh Nuru Khalid Daga Limanci

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ƴan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja, ya dakatar da babban limamin Masallacin Shiekh Nuru Khalid daga Limanci. Sheikh Nuru Khalid a cikin hudubarsa ta ranar Juma’a 1 ga watan Afrilu, ya caccaki gwamnati kan kasa magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya. A cikin hudubar, malamin ya faɗi matakin da ya kamata talakawa su ɗauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na kin fitowa…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Ku Cigaba Da Yi Wa Kasa Addu’o’i – Kiran Gwamna Ga Malamai

Daga Adamu Shehu Bauchi Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi ya ja hankalin shugabannin Addinai da su cigaba da yi wa Jihar Bauchi da Najeriya baki daya addu’a musamman yanzu da kasar ke tunkarar manyan zabubbuka na shekarar dubu biyu da ashirin da uku 2023. Ya yi wannan jawabi ne a wajen taron addu’oi na musamman da hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar ta shirya a sansanin Alhazai na din-din-din dab da filin tashin jiragen sama na kasa da kasa da ya gudana a ranar Jumma’a. Bala yace, “ku…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Masari Ya Bada Umarnin Karantar Da Dalibai Da Hausa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamna Aminu Masari ya umarci malamai a cibiyoyi daban-daban na ilimi a jihar da su fara koyar da yara da harshen Hausa. Masari ya bayar da wannan umarni ne a lokacin kaddamar da wasu litattafai uku da suka shafi wakoki da adabi a kasar Hausa da kuma fassarar kamus na Turanci zuwa harshen Hausa wanda Mande Muhammad ya rubuta. Gwamnan wanda kwamishinan ilimi, Farfesa Badamasi Charanchi ya wakilta, ya bayyana cewa irin wannan tsarin na koyarwa zai taimaka wa yara…

Cigaba Da Karantawa

Kwankwaso Ya Shawarci Matasa Da Shiga Jam’iyyar NNPP

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Najeriya musamman matasa da su shiga jam’iyyar NNPP don dawo da Najeriya da samar da rayuwa mai kyau da ‘yan kasa ke so. Kwankwaso wanda ya yi wannan kiran yayin babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja, ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta shirya fwajen ceto al’ummar kasar. A cewar tsohon gwamnan, sabuwar jam’iyyar za ta tabbatar da ayyukan yi, da ingantaccen ilimi ba tare da yajin aikin ba, da…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 17 A Daren Azumi

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kashe aƙalla mutum 17 a wani hari da suka kai ƙauyuka huɗu na karamar hukumar Anka jihar. Mazauna yankin sun ce mutanen ɗauke da makamai sun farmaki ƙauyen Kadaddaba da tsakar rana, suka buɗe wa mutane wuta. Sun bayyana cewa ba bu wani abu na tsokanar faɗa da yan kauyen suka yi da ya jawo yan ta’addan suka kai harin. Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da…

Cigaba Da Karantawa

Gargadi: ‘Yan Bindiga Na Iya Tarwatsa Najeriya – El Rufa’i

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya ce ‘yan Boko Haram ne suka tsara tare da aiwatar da hari kan jirgin kasa a Abuja zuwa Kaduna wanda ya haifar da rasa rayuka tare da garkuwa da adadi mai yawa na matafiya. Gwamna ya bayyana haka ne a ranar Juma’a lokacin da ya ke yiwa manema labarai bayani kan sakamakon ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa. El-Rufai ya ce harin ya yi sanadi mutuwar aƙalla Fasinjoji takwas da raunatar wasu 40…

Cigaba Da Karantawa

Musulmin Najeriya Sun Tashi Da Azumin Ramadan Yau Asabar

Rahotanni daga fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar dake Jihar Sokoto na bayyana cewar kwamitin duban wata ya sanar da cewa an ga watan azumin Ramadan na shekarar 2022 a wasu sassan ƙasar da yammacin ranar juma’a. Hakan ya tabbatar da cewa yau Asabar 2 ga watan Afrilun 2022 aka tashi da azumin a matsayin 1 ga watan Ramadan na shekarar 1443 bayan Hijira. Sanarwar ganin watan ya zo ne bayan da ƙasar Saudiyya ta sanar da nata ganin watan tun da yammacin ranar ta Juma’a 1 ga…

Cigaba Da Karantawa