An Samar Da Kwararan Matakai Wajen Magance Matsalar Lantarki – Minista

Gwamnatin Nijeriya ta ce an samu nasarar maido da wutar lantarki bayan katsewarta a farkon makon nan, lamarin da ya jefa kasar cikin duhu, sakamamon karancin gas da kuma ayyukan masu fasa bututun dake samar da gas ga manyan tashoshin samar da wutar lantarki. Sanarwa dake dauke da sa hannun Ministan Lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu da aka fitar yau Asabar ta kara da cewa, an samu nasarar gyara bututan gas da aka lalata a babbar tashar lantarki ta Okpai, wanda hakan ya samar karin wutar lantarki da ake samu.…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Dawo Najeriya Daga Birnin Landan

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan shafe akalla kwanaki 12 a kasar Burtaniya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya. Shugaban ya tafi birnin Landan kusan makwanni biyu da suka gabata domin ganawa da masu duba lafiyarsa kamar yadda ya saba a duk shekara. Shugaban ya dawo gida a ranar Juma’a, inda ya samu tarbar wasu daga cikin jiga-jigan gwamnati a fadarsa da ke Abuja. Rahotanni sun bayyana cewar jirgin shugaban kasan ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne…

Cigaba Da Karantawa

Neja: Izala Ta Share Wa ‘Yan Gudun Hijira Hawaye

Rahotanni daga Minna babban Jihar Neja na bayyana cewar Kungiyar Izala ta tallafawa ‘yan gudun hijira a kananan hukumomi 13 dake fama da matsalar tsaro a Jihar. Kungiyar ta bada wannan tallafi ne ga yan gudun hijira dan rage masu radadin da suke fama dashi na rayuwa sakamakon fitintinun ‘yan ta’adda da ya raba su da garuruwan su. Shugaban kungiyar ta jahar Neja Alh Abdullahi Musa Mai Radiyo Shi ya jagoranci kaddamar da wannan gagarumin aiki. Kayayyakin sun haɗa daShinkafa buhu 113Semovita 100Wake buhu 10Masara buhu 5Dawa buhu 1Taliya Caton…

Cigaba Da Karantawa

Buni Ya Yi Watsi Da Batun Tsige Sakataren APC

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC ta ƙasa, Gwamna Mala Buni na jihar Yobe, ya gana da Sakataren kwamitinsa, John Akpanudoedehe. Rahotanni sun bayyana cewar Mai Mala Buni ya gana da Sakataren ne domin yin watsi da takardar dake yawo cewa mambobin kwamitin sun tsige shi daga kujerarsa ta Sakatare. Jam’iyyar APC dai na cigaba da fuskantar rikicin cikin gida tun bayan tafiyar da shugaban ƙasa Buhari ya yi waje duba lafiyar sa.

Cigaba Da Karantawa

Matsalar Lantarki Ce Babbar Matsala A Najeriya – Tinubu

Rahoton dake shigo mana daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa zai farfado da tattalin arzikin Najeriya tare da rage dogaro kan arzikin man fetur idan ya haye karagar mulki a 2023: Dan takaran kujeran shugaban kasan ya ce ya yi niyyar gadar kujerar shugaba Muhammadu Buhari ne don amfanin yan Najeriya, amma ba domin biyan buƙatar kanshi ba. Tinubu yace rashin wutar lantarki ne babban matsala ga cigaban tattalin arzikin Najeriya saboda rashin wuta ke kara farashin kaya,…

Cigaba Da Karantawa

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Doshi Tiriliyan Arba’in – Ofishin Kula Da Basussuka

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ofishin dake kula da bashi a Najeriya ya ce bashin da ke wuyan gwamnati ya karu sosai a 2021. Darakta-Janar ta Ofishin Patience Oniha ta bayyana hakan ta na mai cewa kudin da ake bin Najeriya ya karu daga Naira Tiriliyan 32 a 2020 zuwa Tiriliyan 38 a 2021. Patience Oniha tayi wannan bayani lokacin da ta zanta da manema labarai a Abuja, ta ce wannan ya kunshi bashin gwamnatin tarayya da na jihohi. An yi amfani da wannan…

Cigaba Da Karantawa