Dan Takarar Gwamna Tsohon Babban Hafsan Sojin Sama Ya Ziyarci Bauchi

Daga Adamu Shehu Bauchi Dan’takarar Gwamnan jihar Bauchi, tsohon babban hafsan Sojin sama kuma Jakadan Najeriya a kasar Chadi, Mashal Abubakar Sadiqque ya ziyarci jiharsa ta haihuwa dan’gane da hidimar zaben gama gari dake karatowa a shekarar dubu biyu da ashirin da uku 2023. Jigajigan Yan’siyasar jihar daga bangarori dabam-dabam ne suka tarbe shi a filin tashi da saukan jirage na kasa dake Jihar, musamman yayan Jam’iyyar APC Wanda a karkashin Jam’iyyar ne yake zawarcin kujerar Gwamnan jihar. Jimkadan bayan ya isa gida domin ganawa da magoya bayansa, kana Kuma…

Cigaba Da Karantawa

2023: El Rufa’i Zai Jefa APC Cikin Rudani – APA

Kungiyar APC Political Alliance (APA), ta yi gargadin cewa rigingimun siyasa a jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna wanda suke zargin gwamna Nasir Ahmed El-Rufai na nuna son zuciya wurin tafiyar da mulkin adalci a matsayin sa na shugaba ba mulkin kama karya ba wanda hakan zai sa APC ta rasa kujerar mulkin jihar Kaduna ga jam’iyyun adawa a zaben 2023 dake zuwa. Kungiyar wacce ta kunshi dattawan mashahuran mutane, mata, matasa, da shugabannin masana’antu ‘ya’yan jam’iyyar APC ne kuma masu goyon bayan jam’iyyar APC, ta ce matakin da Gwamna El-Rufai…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: Kalaman Mataimakin Gwamna Gaban Malaman Addini Sun Bar Baya Da Kura

Daga Ibrahim Madugu Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar an shiga rudani biyo bayan wasu kalaman da suka fito daga bakin sabon Mataimakin Gwamnan Zamfara Alh. Hassan Nasiha, a lokacin da Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta jihar Zamfara ta kai masa ziyarar taya murnar samun matsayin Mataimakin Gwamna ranar Alhamis, 10 ga watan Maris, 2022. Da yake mayar da jawabi ga Malaman Addinin, Alh. Hassan Nasiha ya ce “A SHEKARAR 2011 IMANI NE YASA SUKA FAƊI ZAƁE” amma a cewar sa “YANZU BABU…

Cigaba Da Karantawa

Dalilina Na Kwace Filin Jami’ar Ahmadu Bello – El Rufa’i

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin Jihar karkashin jagorancin gwamna Nasiru El Rufa’i ta bayyana dalilinta na kwace fiye da hekta 74 a cikin filin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ABU mai girman hekta 338. A cewar gwamnatin, jami’ar ta sauya takardun mallakar filin ba bisa ka’ida ba, wanda ya ci karo da asalin takardun da gwamnati ta bayar. Gwamnatin jihar ta ce asali tun 1965 aka bayar da takardun ga Northern Veterinary Experimental Station wacce ta koma Kwalejin kimiyar noma da kiwo ta…

Cigaba Da Karantawa

2023: Atiku Ya Roki PDP Ta Sake Ba Shi Dama

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sanar da kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP aniyarsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023, inda ya yi rokon da a sake ba shi dama. Ya bayyana kudirin nasa ne a ranar Talata, yayin wata ganawa da shugabannin Jam’iyyar a Abuja. Atiku wanda ya kasance dan takarar babbar jam’iyyar adawar a zaben 2019, ya roki a sake bashi dama domin ya wakilci PDP a zabe mai zuwa na 2023.…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Uba Sani Ya Bayyana Aniyarsa Ta Zama Gwamna

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa Sanata Uba Sani ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023 dake tafe. Sanata Uba Sani ya bayyana ra’ayin sa na zama gwamnan Kaduna ne a hedikwatar jam’iyyar APC dake Kaduna ranar Talata. Wannan taro ya samu halarcin jigajigan ƴan siyasa da ke jihar musamman ƴaƴan jam’iyyar APC A jawabin da yayi a wajen bayyana burin sa, sanata Uba Sani ya ce, shine ya…

Cigaba Da Karantawa

Babu Gaskiya A Labarin ‘Yan Sanda Za Su Tsunduma Yajin Aiki – Shugaban ‘Yan Sanda

Rahotannin dake shigo mana daga Abuja na bayyana cewar Shugaban ‘yan sanda Usman Alƙali ya mayar da martani ga rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke cewa jami’an ‘yan sanda na shirin zanga-zanga a ranar 26 ga Maris domin neman karin albashi da alawus. Shugaban ‘yan sandan ya bayyana cewa babu dan sandan da zai kaskantar da kansa zuwa ga yin zanga-zanga kan karin albashi saboda suna sane da illar hakan. A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mukaddashin kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya yi watsi da rahoton, yana…

Cigaba Da Karantawa