Adamawa: An Shawarci Iyaye Su Tarbiyyantar Da ‘Ya’yansu Karatun Alkur’ani

An kirayi iyaye musamman mata da su kasance masu nunawa ‘ya’yan su tarbiya da karatun Al qur’ani mai girma tun suna kanana domin samun cigaban karatun Al qur’ani dama tarbiya yadda ya kamata a tsakanin su. Malama Aisha Adamu ce tayi wannan kira a lokacin bikin saukar karatun Al- qur’ani mai girma ƙarƙashin jagorancinta. Wanda aka gudanar a cikin garin Jimeta dake karamar hukumar Yola ta Arewa, fadar gwamatin jihar Adamawa. Malama Aisha tace nunawa yara karatun Al qur’ani mai girma dama nuna musu tarbiya tun suna kanana ya na…

Cigaba Da Karantawa

Rikicin APC: Buhari Ya Gargadi ‘Yan Jam’iyya Kan Nuna Wa Juna Yatsa

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi gargaɗi ga shugabanni da ƴan jam’iyar APC da su daina nuna wa juna yatsa da sa-in-sa a junansu, yayin da jam’iyar ke tunkarar babban taron ta na ƙasa a ranar 26 ga watan Maris. An ruwaito cewa APC ta sake nutsa wa cikin rikici bayan da gwamnoni 19, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai su ka hamɓarar da kujerar shugaban kwamitin riƙo na jam’iyar, Gwamna Mai Mala Buni, inda a ke zargin da umarnin shugaban ƙasa su ka aikata hakan. Daga bisani sai Buhari ya…

Cigaba Da Karantawa

Saudiyya Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Mutane 81

Rahotanni daga birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya na bayyana cewar kasar ta zartar da hukuncin kisa kan mutum 81 a rana ɗaya bayan samunsu da laifukan da suka shafi ta’addanci, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar SPA ya ruwaito. Wannan ya zarta adadin mutanen da aka zartarwa hukuncin kisa a bara. Mutanen sun haɗa da waɗanda aka samu da laifin suna da alaƙa da Al Qaeda da IS da kuma mayaƙan Houthi da ke yaƙi a Yemen. Waɗanda aka kashe suna shirin kai hare-hare a Saudiyya – da koƙarin kashe…

Cigaba Da Karantawa

Yakin Rasha Da Ukraine Zai Haifar Mana Da Annoba – Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya gargadi yan Najeriya cewa kowa yayi tanadi kuma a kwana da shirin tsindumawa cikin karancin abinci da tsananin yunwa nan da watanni biyu masu zuwa. Dangote ya ce dole gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci, masana;antu da noma su zauna a tattauna yadda za akawo karshen wannan matsala . Ya kara da cewa tun yanzu an fara samun hauhawan farashin abubuwa kamar Taki, Masara, Alkama da dai sauran su. ” Za a samu karancin Masara da alkama a duniya saboda…

Cigaba Da Karantawa

Za A Fuskanci Matsananciyar Yunwa A Najeriya – Majalisar Dinkin Duniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya miliyan 19.4 ne za su yi fama da yunwa da barazanar rashin abinci a watannin Yuni zuwa Agustan bana. Hukumar ta yi wannan bincike tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Gona ta Tarayya da wasu Cibiyoyi masu ruwa da tsaki a harkar noma. Rahoton ya yi nazarin matsalar ƙarancin abincin da za a fuskanta da kuma rashin abinci mai gina jiki a yankunan Sahel da Afrika ta…

Cigaba Da Karantawa