Sama Da Mutum 120 Na Goga Wa Cutar Kanjamau – Wata Budurwa

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana yawan mutanen da ta shafa wa cutar kanjamau bayan ta gano tana da cuta mai karya garkuwar jiki a shekarar 2016. Ta yi wannan bayanin ne a Twitter bayan wata ma’abociyar amfani da Twitter ta sanar da yadda take rayuwa da cutar tsawon shekaru uku bayan ta same ta. Ta bayyana cewa ta samu cuta mai karya garkuwar jikin yayin da take da shekaru 21 a duniya kuma yanzu shekarunta 24. “Na samu cutar kanjamau inda da shekaru 21 kuma yanzu shekaru na 24…

Cigaba Da Karantawa

Mai Shadda Zai Angwance Da Jaruma Hassana Muhammad

Furodusa a masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya Bashir Abdulkareem Mai Shadda, zai angwance da amaryarsa jaruma Hassana Muhammad. Za a daura auren ne a unguwar Masallacin Murtala da ke Kano a ranar 13 ga watan Maris kamar yadda Maishadda ya sanar. “Ina farin cikin gayyatar masoya daurin aurena. Wadanda kuma ba za su samu damar zuwa ba, sai a taya mu da addu’a.” Mai Shadda ya rubuta a shafinsa na Instagram hade da katin gayyata a ranar Talata. Jaruma Hassana Muhammadu na daya daga cikin jaruman Kanyywood mata da…

Cigaba Da Karantawa

Kotu Ta Sanya Ranar Saurarar Bukatar Miƙa Kyari Amurka

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar Kotun tarayya dake zamanta a birnin ta zaɓi ranar 23 ga watan Maris, 2022 domin fara tafka mahawara kan bukatar gwamnatin tarayya na miƙa Abba Kyari zuwa Amurka. An ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ofishin Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, ta shigar da bukatar gaban Kotu, ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022. Karar wacce aka raɗa wa, “Neman sahalewar miƙa Abba Kyari ga ƙasar Amurka,” na ɗauke da kwanan wata dai-dai da ranar da aka shigar da ita 2 ga watan Maris.…

Cigaba Da Karantawa

Kebbi: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji Da ‘Yan Sanda

Rahotanni daga jihar Kebbi na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro a kalla 19 a wani hari da suka kai a ƙauyen Kanya da ke cikin karamar hukumar Danko-Wassagu. Maharan sun je ne a kan babura a lokacin da mataimakin gwamnan Kebbi ke ziyara a ƙauyen a ranar Talata. Mataimakin gwamnan Samaila Yombe Dabai, ya shaida cewa dakarun tsaron sun fafata ne da maharan, amma bai faɗi yawan jami’an da aka kashe ba. Mutanen da suka mutun sun haɗa da sojoji 13 da ƴan sanda biyar…

Cigaba Da Karantawa

Kano: DSS Ta Gayyaci Mukarraban Ganduje

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci wasu manyan na hannun-daman gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje. Bayanan da muka samu sun nuna cewa mutanen sun kai kansu gaban DSS bisa zarginsu da hannu a dabar siyasa. Kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar ta Kano, Murtala Sule Garo, wanda ya tabbatar wa BBC wannan labarin, ya ce ba ya cikin manyan jami’an gwamnatin jihar da suka mika kansu ga DSS. A tattaunwarsa da BBC, Fa’izu Alfindiki, shugaban karamar hukumar Birnin Kano, ya ce…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ne Ya Bada Umarnin Tsige Mai Mala Buni – El Rufa’i

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya goyi bayan cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko na Jam’iyyar APC. Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana haja a hirar da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi ranar Talata, dangane da danbarwar da ake ciki a shugabancin APC. Malam Nasiru El Rufai ya ƙara da cewar gwamnan jihar Neja Sani Bello ya samu goyon bayan Buhari da kuma gwamnonin APC 19. Sannan ya…

Cigaba Da Karantawa