Legas: An Shiga Farautar Wadanda Suka Yi Kyautar Fetur A Gidan Biki

Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar gwamnatin Jihar ta ce tana bincike kan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta inda wasu ke raba man fetur a cikin jarkuna a matsayin kyautar halartar biki. Kwamashinan Yaɗa Labarai na jihar Legas, Gbenga Omotoso, ya ce “shakka babu wannan lamarin abin haɗari ne kuma zai iya jawo rasa rayuka da dukiyoyi”. A ‘yan awannin da suka gabata ne bidiyon ya ɓulla, inda aka ga jarkunan fetur masu lita 10 a jere da za a raba wa mahalarta bikin. An…

Cigaba Da Karantawa

Kurkuku Ya Kamaci Wasu ‘Yan Takarar Shugabancin Kasa – Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce wasu masu burin zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ya kamata a ce suna gidan yari idan da hukumomin da ke yaƙi da rashawa a Najeriya suna aikinsu yadda ya dace. Tsohon shugaban ya faɗi haka ne a wani babban taron ƙara wa juna sani da aka gudanar a Abeokuta jihar Ogun domin bikin cikarsa shekara 85 da haihuwa, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito. “Na kalli wasu daga cikin mutanen da ke yawo da kuma wadanda mutane ke yawo da su. Idan…

Cigaba Da Karantawa

Kurakuran PDP Ne Silar Zaman Buhari Shugaban Kasa – Saraki

Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya alakanta hawan Buhari da jamiyyar APC mulki da kura-kuran da jam’iyyar PDP ta tafka. Saraki ya bayyana matsayinsa ne ta hannun Farfesa Iyorwuese Hagher, shugaban kungiyar yakin neman shugabancinsa, lokacin da ya jagoranci tawagarsa zuwa Dutse babban birnin jihar Jigawa don tattaunawa da masu ruwa da tsaki na PDP a jihar. Ya ce mafita kwaya daya da ya rage ma jam’iyyar adawar shine ta yi aiki don kwato shugabancin kasar domin kawo ainahin chanjin da kasar ke muradi. Tsohon shugaban majalisar dattawan na…

Cigaba Da Karantawa

2023: Tinubu Ya Cancanci Shugabancin Kasa – Sarkin Katsina

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, ya nuna goyon bayansa ga takarar Sanata Ahmed Bola Tinubu na shugabancin kasa. Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tarbar wata tawagar kungiyoyin Arewa masu goyon bayan takarar shugabancin kasar Tinubu da suka kai masa ziyara a fadarsa a ranar Juma’a a Katsina. Sarkin ya ce Tinubu ya cancanta kuma zai shayar da ƴan Najeriya romon demokradiyya, “Tinubu mutum ne da zai iya ceto yan Najeriya daga matsalolin tsaro, tattalin arziki da zamantakewar. “Na…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Mahaukaciyar Gobara Ta Yi Barna A Hukumar SEMA

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar wata Mahaukaciyar Gobara da ta tashi ranar Jumu’a da yamma a siton hukumar kai agajin gaggaywa SEMA ta lakume kayayyakin da suka kai darajar miliyan N18 da rabi. An ruwaito cewa wutar ta yi wannan aika-aika ne a Siton SEMA dake Mariri, ƙaramar hukumar Kumbutso dake jihar Kano. Sakataren hukumar SEMA, Dakta Saleh Jili, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin hira da manema labarai a Kano ranar Jumu’a. Ya ce lamarin ya auku ranar Jumu’a da karfe 1:00 na rana…

Cigaba Da Karantawa

Ba Za Mu Iya Biyan Buƙatun ASUU Ba – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan alƙawurran da Gwamnatin Tarayya ta sha yi wa Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta biya buƙatun su domin su daina yajin aiki, a yau kuma gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da kuɗaɗen da za ta iya biya wa malaman jami’o’i buƙatun da suke nema ɗin. Ministan Ƙwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin da Gidan Talabijin na Channels ke hira da shi a ranar Alhamis. Kafin tafiyar ASUU yajin aiki makonni biyu da…

Cigaba Da Karantawa

Dawowar Buhari Najeriya: Bai Shafi Tafiyar Shi Landan Ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar, Shugaban ƙasa Buhari ya dawo Najeriya bayan tafiyar da ya yi kasar Kenya, da fari an tsara Shugaban zai wuce Birnin Landan daga Nairobi domin ganin Likita. Sai dai Fadar Shugaban ƙasa ta yi ƙarin haske akan dawowarsa inda tace Tafiyar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zuwa Landan domin ganin likita ta na nan a ranar Lahadi mai zuwa. Mutane sun yi mamakin ganin shugaban ƙasan ya dawo gida Najeriya ranar Jumu’a, maimakon zarcewa Birnin Landan kamar yadda fadarsa ta…

Cigaba Da Karantawa