Da Dumi-Dumi: An Yi Tankade A Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa fitaccen ɗan jarida, kuma tsohon ɗan majalisar tarayya daga Jigawa, Sani Zorro, hadimin uwargidan sa Aisha Buhari. Sani Zorro zai yi aiki a ofishin uwargidan shugaban kasa a matsayin babban mai taimaka mata kan harkokin hulɗa da jama’a da tsare-tsare. Bayan haka, a cikin sanarwar wanda Garba Shehu ya fidda ranar Asabar, shugaba Buhari ya amince da a sauya wa wasu manyan hadimai da ke aiki a ofishin uwargida Aisha wuraren aiki. An…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Magajin Garin Sokoto Ya Kwanta Dama

Rahotannin dake shigo mana yanzu haka daga birnin Sokoto na bayyana cewa Allah Ya yi wa Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Marafa Danbaba rasuwa yau Asabar a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya. Wani babban aminin marigayin ne ya tabbatar da rasuwar Magajin Garin na Sokoto a wata tattaunawa da gidan Rediyon BBC Hausa ya yi dashi. Ana sa ran za a yi janai’zar Marigayin anjima a babban Masallacin juma’a na Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dake birnin Sokoto. Marigayin ya kasance ɗa ga Aishatu Ahmadu Bello, wadda ita ce babbar ɗiyar…

Cigaba Da Karantawa

Sai ‘Yan Mata Sun Bada Kansu Kafin Ake Saka Su A Fim – Sarkin Waka

Shahararren mawakin zamani Naziru Sarkin Waka ya yiwa jagororin Hausa film wankin babban bargo, inda ya bayyana halayyar tsarin ‘yan jari hujja da danniya da lalata da akeyi a Masana’antar Naziru yace Wallahi ‘yan Hausa film ba Allah a ranku, ya fadi hakane sakamakon hiran da BBC tayi da wata tsohuwar jaruma a Masana’antar Hausa film Ladi Cima inda tace bata samun abinda ya wuce Naira dubu 10, shine sai daraktocin film suka mata caa suna raddi a gareta Sarkin Waka yace kamar Ali Nuhu da Falalu Dorayi karya suke…

Cigaba Da Karantawa

Za A Fara Biyan Mata Masu Juna Biyu Albashi A Jigawa

Rahotanni daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewa Gwamnatin Jihar ta bayyana cewa komai ya kankama don fara biyan mata masu juna biyu sama da 5000 kudi dubu biyar-biyar a duk wata. Mataimakain Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi, ya bayyana haka a yayin wata ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar. Namadi yace jihar ta bullo da shirin ne domin ya taimaka wa mazauna karkara don su rika zuwa awon ciki a asibiti kafin haihuwa. Ya ce gwamnatin Muhammad Badaru ta sanya wannan kudi cikin kasafin…

Cigaba Da Karantawa

Zan Taimaki Matasa Wajen Samun Mukamai A APC – Buhari

Mai girma Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari rana Jumu’a, ya tabbatar wa matasan APC cewa zai goyi bayan zakakurai daga cikinsu su ɗare manyan muƙamai a babban taron APC dake tafe a ranar 26 ga watan Fabrairu. Kazalika Buhari ya umarci shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, su tabbatar an saka matasa masu hazaka a gwamnatinsa. Bayan haka Shugaba Buhari ya roki matasan APC su yi aiki tukuru wajen tabbatar da jam’iyya ta cigaba da rike kujerun gwamnonin jihar Ekiti da Osun da zaɓen…

Cigaba Da Karantawa

Zaben Abuja: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Jaddada Dokar Hana Zirga-Zirga

Rahoton dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta bada sanarwar tsaurara matakan hana zirga-zirga a daidai lokacin da ake gudanar da zabukan kananan hukumomi a birnin. Sanarwar da rundunar ta fitar ya bayyana cewar za a hana dukkanin wata zirga-zirga a birnin tun daga misalin karfe takwas na safe har zuwa karfe uku na rana domin samun gudanar da zabukan kananan hukumomi a yankin a ranar yau Asabar. Rundunar ta ƙara da cewa ɗaukar matakin hakan ya biyo bayan rahoton da suka…

Cigaba Da Karantawa

Kotun Koli Ta Yi Fatali Da Dokar Da Buhari Ya Sanya Wa Hannu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Kotun Ƙoli ta yi watsi da doka mai lamba goma wadda aka fi sani da “Presidential Executive Order No. 00-10 of 2020” wadda ta bayar da umarni ga babban akanta janar ya cire kuɗaɗe kai tsaye daga alawus-alawus na jihohi domin bai wa ɓangarorin shari’a. Alƙalan Kotun Ƙolin duka waɗanda suka yi zama a ranar Juma’a sun amince da cewa dokar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi ta saɓa ƙa’idar kundin tsarin mulki. A bara ne babban lauyan…

Cigaba Da Karantawa