Jigawa: Matashi Dan Shekara 25 Ya Rataye Kanshi

Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta ce wani matashi dan shekara 25 ya kashe kansa a karamar hukumar Taura da ke jihar. Kakakin Rundunar Ƴan sandan Jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Talata a Dutse, babban birnin jihar. Shiisu ya ce matashin ya yi amfani da wandonsa ne ya rataye kanshi a jikin wata bishiya a jiya Litinin. Ya ce, matashin, wanda a baya aka ce ya ɓace, an same shi yana rataye a jikin bishiya a wani…

Cigaba Da Karantawa

Rashin Lafiya Ne Silar Mutuwar Abiola – Abdulsalami

Tsohon Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojan Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya yi hira ta musamman da gidan talabijin na Trust TV, inda ya karyata cewa guba ce ta kashe Mashood Abiola tsohon dan takarar shugabancin kasa a shekarar 1993. A cewar Abubakar, rashin lafiya ne ya kashe Abiola, akasin abin da ake fada cewa guba aka ba shi a tsare, shekaru biyar bayan ya yi takarar shugaban kasa. An ruwaito Abdussalami yana cewa ya na dariya saboda akwai rade-radi nan-da-can cewa mu muka hallaka MKO Abiola alhali babu kamshin…

Cigaba Da Karantawa

Kotu Ta Bada Umarnin Kamo Tsohuwar Ministar Mai Duk Inda Take

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta bada umarnin kamo tsohuwar ministan Man Fetur, Diezani Alison-Madueke a duk inda ta ɓuya a duniya. Alkalin kotun, mai Shari’a Bolaji Olajuwon, shi ya bada umarnin ranar Litinin, biyo bayan bukatar da lauyan hukumar yaƙi da cin hanci, (EFCC), Farouq Abdullah, ya gabatar. A baya tsohuwar alƙalin kotun, Ijeoma Ojukwu, ta yi watsi da bukatar kamo Diezani, saboda gazawar EFCC wajen tabbatar da sammacin da aka aike wa tsohuwar ministan. “A gani na sammacin…

Cigaba Da Karantawa

2023: Tinubu Ya Fi Kowa Cancanta – Yakasai

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Alhaji Tanko Yakasai, wani dattijon kasa daga jihar a ranar Lahadi, 23 ga watan Janairu ya bayyana goyon bayansa ga dan Kudu ya maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshen wa’adinsa a 2023. An ruwaito cewa, dattijon dan shekaru 96 da haihuwa, ya ce ba zai zama adalci ba a ce yankin Arewa ya ci gaba da yin mulki duk da yunkurin da ‘yan Kudu ke yi na neman kujerar shugabancin kasa. Dattijon ya ce a tsawon shekarun da…

Cigaba Da Karantawa

Kisan Hanifa: Ba Zan Bata Lokaci Wajen Sa Hannun Zartar Da Hukunci Ba – Ganduje

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar yace ba zai bata lokaci ba wajen zartar da hukuncin kashe Abdulmalik Tanko, idan aka kawo shi kan teburinsa. A ranar Litinin an ruwaito cewa gwamnan ya yi alƙawarin bin dokar da tsarin mulki ya tanadar wajen zartar da hukuncin kisa kan Tanko, bayan kotu ta tabbatar. Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya tare da mataimakinsa, Nasuru Yusuf Gawuna, shugaban masu rinjayi na majalisa, Labaran Abdul da ƙusoshin…

Cigaba Da Karantawa

Zargin Sace Kudin Tallafi: Gwamna Bala Ya Yi Karya – Ma’aikatar Jin Kai

Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana wani iƙirari da Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi cewar wai jami’an gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa sun sace naira biliyan 1 “a kan idon Shugaba Muhammadu Buhari” na Shirin Tallafin Rage Fatara (SIP) wanda ma’aikatar ke gudanarwa da cewar ƙarya ce maras makama. Wasu kafafen yaɗa labarai sun kuma ruwaito gwamnan ya na faɗin cewa “cin hanci da rashawa ya riga ya ruguza shirin tallafin NSIP na Gwamnatin Tarayya, sannan ya ƙalubalanci gwamnatin da ta…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin Janye Tallafin Mai

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar Harkokin kudi Zainab Ahmed ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta janye shawarar da ta dauka a baya na cire tallafin mai a cikin wannan shekara. Minista ta ce ganin yadda rayuwa yayi tsanani ba zai yiwu a ce za a cire tallafin man domin talakawa zasu dada fadawa cikin gungurmin talauci ne wanda dama suna fama ne da ita. A dalilin haka gwamnati ta wancakalar da waccan shawarar, ba za ta cire tallafin mai a watan Yuli ba kamar yadda ta…

Cigaba Da Karantawa