Cutar Lassa Ta Zama Annoba A Najeriya – Masana

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Masana na ci gaba da nuna damuwa kan rahoton da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta fitar, wanda ta ce mutum 96 sun kamu da cutar zazzabin Lassa cikin kananan hukumomi 27 a jihohin kasar. Dr Salihu Ibrahim Kwaifa, kwarraren likita ne a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya sahida wa BBC cewa adadin ka iya wuce haka idan aka fadada bincike. Likitan ya ce,”Akwai tashin hankali saboda idan da har za a zurfafa bincike to ko shakka ba…

Cigaba Da Karantawa

Majalisa Za Ta Binciki Makaman Da Suka Yi Batan Dabo Hannun ‘Yan Sanda

Majalisar Wakilan Najeriya za ta gudanar da bincike kan zargin batan makamai da suka kunshi bindigogi da albarusai 178,459 daga ma’adanar ‘yan sandan kasar. Majalisar ta kuma yi kira ga Sufeto Janar na ‘yan sandan da ya dauki matakan gaggawa wajen gano wadanda suke da hannu wajen batan makaman. ‘Yan Majalisar sun bayar da umarnin ne a zaman da suka yi jiya Alhamis, bayan da rahoton shekara ta 2019 na Ofishin Babban Mai Bincike na Kasar ya ambato zargin batan makaman, kamar yadda jaridun kasar suka yi ta rahoton a…

Cigaba Da Karantawa

Borno: ISWAP Sun Yi Ta’asa A Garin Chibok

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar masu iƙirarin jihadi da ake zargin ‘yan ƙungiyar ISWAP ne sun kashe mutum biyu tare da sace wasu yara 20 a kusa da garin Chibok na Jihar Borno ranar Alhamis. Wani shugaban yankin ya faɗa wa manema labarai cewa maharan sun afka wa garin Piyemi, inda suka yi awon gaba da mata 13 da maza bakwai. A cewar mazauna yankin, mayaƙan na Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun afka wa garin ne da rana cikin kakin sojoji suna harbe-harbe…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Za Mu Tabbatar Doka Ta Yi Aiki Akan Makasan Hanifa – Ganduje

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da sanya ido sosai tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifi a yin garkuwa da kisan gilla da aka yi wa Hanifa Abubakar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ya fitar. Gwamnan ya ce tuni matakan da aka dauka a lamarin sun fara aiki, ciki har da rufewa da kuma janye…

Cigaba Da Karantawa

Matsalar Tsaro Zai Haifar Mana Cikas A Babban Zabe – INEC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar matsalar tsaro yayin da zaben 2023 ke ƙaratowa. Yakubu ya yi wannan furuci ne a wurin taron kwamitin tsaro na haɗin guiwa (ICCES), wanda ya gudana a hedkwatar hukumar INEC dake Abuja ranar Juma’a. Shugaban INEC ya kuma yaba wa hukumomin tsaro bisa namijin kokarin da suka yi wajen tabbatar da tsaro yayin zaben gwamnan jihar Anambra. Sai dai yace yawaitar matsalar tsaro a sassan Najeriya, wata…

Cigaba Da Karantawa