Bauchi: Mutanen Guru Sun Firgita A Tunanin Rashin Adalci Daga Gwamnati

Daga Adamu Shehu Bauchi Al’ummar Kauyen Guru dake cikin karamar hukumar Bauchi dab da fadar Jihar sun shiga cikin zullumi da fargaba cewa Gwamnati baza tayi masu adalci ba wajen biyansu kudaden filayensu da Sojojin Najeria suke shirin kwacewa a hannun su tun bayan shekaru dari Uku da zamansu a wan nan wuri, Sunyi wan nan furucin ne a lokacin da suke ganawa da jami’an Gwamnati wanda Gwamnan Jihar Bala Mohammed ya aika da nufin su tattauna da mutanen yankin, akan wan nan batu amma abunya faskara. Shugaban tawagar kuma…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: Fintiri Ya Rantsar Da Shugabannin Rikon Kananan Hukumomi

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya rantsar da Shugabannin riko na kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jihar baki daya. An dai gudanar da bikin ratsuwarne a dandalin Mahmudu Ribadau dake Yola fadar gwamnati jihar Adamawa. Da yake rantsar da sabbin shugabannin riko na kananan hukumomi gwamna Fintiri ya kirayi sabbin shugabannin da su maida hankalinsu wajen gudanar da ayyukan cigaban jihar tare da shawartansu da suyi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro wanda hakan zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya. Ya kuma kirayi magoyan Jam’iyar…

Cigaba Da Karantawa

Duk Wanda Ya Riki Al-Kur’ani Ba Zai Tabe Ba – Sheikh Dahiru Bauchi

Daga Adamu Shehu Bauchi Shahararren Malamin nan Sheikh Dahiru Usman Bauchi yaja hankalin Iyaye da yayansu su riki Alkur’ani Mai Girma ta wajen haddace shi da Kuma sanin abinda yake koyarwa don samun al’umma mai inganci da kuma Ladan da bashi da iyaka a wajen Allahu subahanahu-wata’ala. Shaihin Malamin yayi wan nan Jan hankalin ne a lokacin da yake dana Uwar gidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Mohammed a matsayin Garkuwar masu haddan Alkur’ani ta Jihar Bauchi a fadar gidansa tare da jikan Manzon Allah (S.A.W) a kusa dashi…

Cigaba Da Karantawa

Na Jima Ina Karin Kumallo Da Naman Mutane – Aminu Baba Fitaccen Dan Kasuwa A Gusau

Alhaji Aminu Baba, fitaccen dan kasuwan nan da ke sana’ar motoci da sauran ababen hawa a kamfanin Aminchi Motors Gusau, Jihar Zamfara, ya bayyana munanan ayyukan sa. Baba, wanda ‘yan sanda suka kama, ya amsa laifin ci da sayar da sassan jikin mutane ga wasu da ba a san ko su waye ba. An kama shi ne a makon da ya gabata bisa laifin kashe wani yaro dan shekara 9 a Gusau. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Ayuba N Elkanah, ya ce wanda ake zargin yana da mata uku da…

Cigaba Da Karantawa

Legas: Hukumar EFCC Ta Yi Nasarar Damke Janar Na Bogi

Labarin dake shigo mana daga Birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewar Hukumar EFCC ta kama wani sojan bogi mai muƙamin Manjo Janar inda aka kama shi bisa zargin zamba ta naira miliyan 270. Hukumar ta EFCC ta kama Bolarinwa Oluwasegun wanda ya yi iƙirarin cewa Shugaba Buhari ya zaɓe shi a matsayin shugaban sojojin ƙasa na Najeriyar. Mista Bolarinwa ya roƙi wani kamfani na Kodef Clearing Resources da ya ba shi kuɗi domin a tabbatar da shi a matsayin shugaban. Haka kuma ana zarginsa da yin wata takarda…

Cigaba Da Karantawa

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Tir Da Rikicin Filato

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan baya-bayan nan da aka yi a Jihar Filato inda ya ce bai kamata yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimmawa ba tsakanin Fulani da Irigwe ta shashance ba. A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya nuna rashin jin daɗinsa kan kashe-kashen da aka yi a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Filato inda shugaban ya buƙaci al’ummomin yankin da kuma musamman majalisar da…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Sojoji Sun Ceto Mutum 26 Daga Hannun ‘Yan Bindiga

A ranar Laraba ne Rundunar Sojin sama ta bayyana cewa ta ceto mutum 26 da aka yi garkuwa da su a Kaduna. Kakakin rundunar Edward Gabkwet ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a Abuja. Gabkwet ya ce sojojin sun ceto wadannan mutane yayin da suke sintiri a babban titin Birnin Gwari zuwa Kaduna. Ya ce bincike ya nuna cewa mutanen matafiya ne daga Birnin-Gwari zuwa Kaduna,wasu kuma daga Minna suke da jihar Kano. “Mutanen sun bayyana wa sojojin cewa gungun masu garkuwa da…

Cigaba Da Karantawa

Siyasar Kano: Ganduje Ya Sake Shan Kasa A Kotu

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar da ɓangaren Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na jamiyyar APC ya gabatar cewa ta jingine hukuncin da ta yi, wanda ya tabbatar da zaben shugabannin jamiyyar da tsagin tsohon Gwamna Senata Ibrahim Shekarau ya gudanar. Tun da farko, kotun ta bai wa tsagin Sanata Shekarau gaskiya, amma sai tsagin Gandujen ya nemi ta sake nazarin hukuncin da ta yi. Kotun ƙarƙashin Mai Sharia Hamza Muazu, ta ƙi amincewa da bukatar da tsagin Gwamna Ganduje ya gabatar saboda ba shi da…

Cigaba Da Karantawa

Za A Fahimci Rawar Da Muka Taka Bayan Mun Bar Mulki – Shugaban Majalisa

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana cewa mafi yawan ‘yan Najeriya na kwana da tashi cikin farin ciki da ‘yan majalisa. Wannan farin cikin kuwa, jin daɗi ne da su ke yi ga mulkin Shugaba Muhammadu Buhari. Lawan ya ce sai ma bayan sun kammala wa’adin mulkin su ne akasarin ‘yan Najeriya za su riƙa santin rubutawa da furta kalaman alheri kan Majalisar Dattawa da ta Tarayya, dangane da ɗimbin nasarorin da suka samar. Lawan ya yi wannan bayani ne a wurin wani taron taya shi murnar cika shekaru…

Cigaba Da Karantawa