Katsina: Masari Ya Sanya Ranar Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina, Malam Ibrahim Bako, ya bayyana a ranar Talata cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022. Bako ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Katsina. Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar Talata ne aka fara gudanar da gangamin yakin neman zaben. Bako ya ci gaba da cewa, “Za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Katsina a ranar Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022, yayin…

Cigaba Da Karantawa

Kisan Zamfara: Buhari Ya Tura Wakilai Yin Jaje

Labarin dake shigo mana daga Jihar Zamfara na bayyana cewar Wakilan gwamnatin tarayya sun dira Gusau, babban birnin jihar ranar Laraba, domin jajantawa gwamnatin jihar bisa harin yan bindiga na kwanan nan. An ruwaito cewa tawagar wakilan karkashin jagorancin Ministan tsaro, Bashir Magashi, ta kunshi, ministan ayyukan jin kai, Sadiya Umar Farouq, da kakakin Buhari, Malam Garba Shehu. Sauran mambobin tawagar sun haɗa da, ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi, mai bada shawara kan tsaro, Babagana Monguno, da kuma Sufeta janar na yan sanda, Usman Baba. Idan masu karatu za…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Kawar Da Yunwa Tsakanin Dalibai A Bana – Ministar Jin Kai

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa majalisar dinkin duniya ta shirya hada kai da ita wajen inganta shirin ciyar da dalibai a makarantun firamaren Najeriya. Ministar tallafi da jin dadin jama’a, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan a jawabin da hadimarta, Halima Oyelade, ta fitar ranar Laraba a Abuja. Hajiya Sadiya ta ce wannan sabon hadin kai da shirin abincin duniya WFP na majalisar dinkin duniya zai taimaka wajen magance matsalar yunwa cikin yara. “WFP na bada goyon baya ta hanyar bada gudunmuwar…

Cigaba Da Karantawa

Neja: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 19 A Masallaci

Labarin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar Shugaban karamar hukumar Mashaegu a jihar Alhaji Alhassan Isah, ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 19 tare da yin garkuwa da 15 a Mazakuka, Kulho, Adogon Malam da kewaye. Shugaban karamar hukumar ya bayyana hakan ne rsnar Talata 11 a lokacin da ya gurfana gaban kwamitin bincike na shari’a da gwamnatin jihar ta kafa kan kashe-kashen. Ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutane 19 a cikin masallaci yayin harin da suka kai ranar 25 ga watan Oktoba…

Cigaba Da Karantawa

Mayakan ISWAP Sun Fi Boko Haram Hatsari – Zulum

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Farfesa Umara Babagana Zulum, Gwamnan jihar ya ce mayakan ta’addanci ISWAP sun fi na Boko Haram miyagun makamai, don haka dole a dakile su da gaggawa. Gwamnan ya yi jawabin ne yayin da ya tarbi mambobin kwamitin majalisar dattawa na kula da harkokin sojoji karkashin jagorancin Ali Ndume. Shugabannin kwamitin sun ziyarci Gwamna Zulum a Maiduguri, babban birnin jihar domin duba irin cigaban da aka samu a fannin samar da tsaro. Zulum Yayi jinjina ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da…

Cigaba Da Karantawa