Kano: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Mahaifiyar Dan Majalisa

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun ɗauke mahaifiyar ɗan majalisar Kano, mai wakiltar Mazaɓar Ƙaramar Hukumar Gezawa, Alhaji Isyaku Ali Ɗanja. Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na dare a jiya Talata a garin Gezawa, inda su ka karya kofar gidan su ka yi awon-gaba da ita. Da ya ke bada bayanin yadda lamarin ya faru, Ɗanja ya ce ƴan bindigar sun nemi mahaifiyar ta sa da ta buɗe musu kofa amma sai ta ƙi buɗewa.…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: Fintiri Ya Nada Shugabannin Rikon Kananan Hukumomi

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bayar da sanarwar nadin shuwagabanin rikon kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jihar ta Adamawa. Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na Gwamnan Hunwashi Wanasiko ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a Yola. Nadin shugabanin rikon dai na zuwane bayan da waadin shugabanin kananan hukumomin ya kare tun a ranan 8-12-2021. Wanda kuma majalisar dokokin jihar ta Adamawa ta amincewa gwamnan nada shugabanin riko na kananan hukumomin. Gwamna Fintiri ya taya wadanda suka samu mukamin murna…

Cigaba Da Karantawa

Gasar Nahiyar Afirka: Najeriya Ta Lallasa Masar Da Ci Daya Mai Ban Haushi

Najeriya ta doke Masar da ci 1-0 a rukunin D na gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta 2021. Dan wasan Najeriya wanda ke buga wasa a Leicester City Kelechi Iheanacho ne ya zura kwallon a minti 30 da soma wasa. Wasan shi ne mafi zafi kawo yanzu saboda girman ƙasashen a tarihin gasar cin kofin Afirka An yi fafatawar ne a birnin Garoua na Kamaru da misalin ƙarfe huɗu na yamma agogon Najeriya da Kamaru.

Cigaba Da Karantawa

Mawaki Ali Jita Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Kano

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na nuna cewa yayin da jama’a ke ci gaba da hasashen yadda babban zaben kasar na 2023 zai kasance, an gano wani fostan yakin neman zabe na shahararren mawakin nan na masana’antar shirya fina-finai na Kannywood, Ali Isa Jita. Fostan wanda abokiyar sana’arsa Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na Instagram, ya nuna cewa mawakin zai fito takarar kujerar gwamnan jihar Kano ne a zaben na 2023. Sai dai kuma babu suna ko tambarin wata jam’iyyar siyasa a cikin hoton wanda ke dauke…

Cigaba Da Karantawa

Ina Goyon Bayan Tsarin Karba-Karba – Shehu Sani

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsohon dan majalisa da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya goyi bayan mulkin karba-karba don adalci samun da daidaito. Ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Gidan Talabijin na Channels yayi da shi ranar Talata dangane da batun siyasar Najeriya a lokacin da shekarar zaɓe ta 2023 ke ƙara tinkarowa. Ra’ayin Sanatan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara kan wanda zai gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda…

Cigaba Da Karantawa

Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Ernest Shonekan Ya Mutu

Allah Ya yi wa tsohon shugaban rikon kwarya na Najeriya Cif Ernest Shonekan rasuwa kamar yadda rahotanni da dama a kasar suka tabbatar.. Cif Shonekan ya mutu ne a wani asibiti a birnin Legas ranar Talata, kamar yadda rahotannin suka nuna. Tsohon shugaban rikon kwaryar ya mutu ne yana da shekara 85 a duniya. Cif Shonekan ne shugaban gwamnatin rikon ƙwaryar Najeriya daga tsakanin 26 ga watabn Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993. Marigayi Janar Sani Abacha wanda shi ne Sakataren Tsaro na kasar a lokacin, ya hambarar da…

Cigaba Da Karantawa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tofin Allah Tsine Da Kisan Zamfara

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da aka kai a karshen mako a jihar Zamfara da ke Najeriya inda aka kashe fararen hula da dama. Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawunsa, Stephane Dujarric, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu. Rahotanni sun bayyana cewa, kimanin mutane 200 ko sama da haka ne aka kashe a kauyukan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, yayin da wasu ‘yan bindiga suka…

Cigaba Da Karantawa