Bani Da Burin Da Ya Wuce Zama Shugaban Kasa – Tinubu

Tsohon gwamnan Legas, kuma jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya ce ya faɗa wa shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasar a zaɓen 2023. Ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin. A cewar Tinubu “na faɗa wa Shugaba Buhari aniyata, ban ji abun da ba shi na yi tsammanin ji daga gare shi ba, ya ƙarfafa min guiwa kamar yadda dumokuraɗiyya ta ba ni dama, amma har yanzu…

Cigaba Da Karantawa

Osinbajo Ya Wakilci Buhari A Taron ECOWAS

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Oisnbajo ya tafi Accra babban birnin ƙasar Ghana domin wakiltar Shugaba Muhammadu Buhari a wani taro na musamman da Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta shirya. Mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar Laolu Akande ne ya fitar da sanarwar inda ya ce shugabannin ƙasashen yammacin Afrika za su tattauna a yayin taron kan batun siyasar ƙasar Mali. Osinbajon ya tafi tare da ƙaramin ministan harkokin waje na Najeriya Ambasada Zubairu Dada, haka kuma ana sa ran za su dawo a…

Cigaba Da Karantawa

Zulum Ne Silar Nasarar Da Muke Samu A Yaki Da Boko Haram – Rundunar Soji

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Kwamandan runduna ta 7 na hukumar sojojin Najeriya, Manjo Janar, A.A. Eyitayo, ya bayyana cewa ba tare da roko ba, Zulum ya tallafawa sojoji a lokuta da dama. Kwamandan ya yi wannan furucin ne yayin da gwamnan ya kai ziyara hedkwatar sojojin dake Maiduguri ranar Lahadi. Rahotanni sun bayyana cewa Zulum ya halarci taro na musamman da sojojin suka shirya domin taya GOC murnar ƙarin girman da ya samu zuwa Manjo Janar. Kwamandan sojojin yace: “A lokuta…

Cigaba Da Karantawa

Babu Maganar Sulhu Tsakanina Da Ganduje – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta wasu raɗe-raɗi da ke yawo da ke bayyana cewa yana tattaunawa da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje don yin sulhu. Yayin wata hira da Channels TV da yammacin ranar Lahadi. Kwankwaso ya ce ya ji daɗin ziyarar ta’aziyyar da Ganduje ya kai masa kwanakin baya, amma bayan wannan ziyara ta gaisuwa babu wata magana da ake yi a bayan fage dangane da yin sasantawa. Ya hakaito yadda alaƙarsa ta kasance da Gandujen a baya tun lokacin da ya yi mata…

Cigaba Da Karantawa

2023: Kuyi Watsi Da Batun Addini Da Kabila Ku Zabi Cancanta – Sanusi

Khalifan Tijjaniyya na Najeriya Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci wadanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a su je su yanki katin zaɓe gabanin babban zaben 2023. Yana magana ne a wajen taron shekara-shekara na tunawa da ranar haihuwar mazon Allah Annabi Muhammad SAW a garin Lokoja. Sanusi ya yi kira ga jama’a idan zaɓen ya zo su zaɓi shugabanni na gari ba tare da la’akari da siyasa ko addini ba. “Idan matasanmu suka samu aikin yi, tattalin arzikin kasar baki daya zai inganta. Mafi mahimmanci, mu ba jam’iyya ba ce, amma ba…

Cigaba Da Karantawa