Zan Gyara Kwamacalar El Rufa’i Idan Na Zama Gwamna – Shehu Sani

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a zaɓen 2023. Yayin hira da wani gidan rediyo a jihar, sanatan ya yi alkawarin wanke abun da ya kira ”tabargazar gwamnan jihar mai ci Nasir El-Rufa’i” idan ya yi nasara. ”Duk wanda ya musguna wa jama’a ya ƙuntata musu bai cancanci ya samu kowacce irin dama ba, domin duka addinanmu sun girmama ɗan adam”. Shehu Sani ya ƙara da cewa a yanzu…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Damke WandaYa Kashe Matarshi Ta Hanyar Daba Mata Wuka

A yanzu haka rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa tana tsare da wani magidanci mai suna Muhammed Alfa dan shekaru hamsin da bakwai da haihuwa wanda yake zaune a cikin kauyen Lande B a karamar hukumar Gombi dake bisa zarginsa da daɓawa tsohuwar matarsa wuka wanda kuma yayi sanadiyar mutuwarta. Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Yola. Sanarwa ta bayyana cewa matar mai suna Hamsatu ta gamu da ajalintane biyo bayan takaddama…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Antaya Daji Da Tsala-Tsalan ‘Yan Mata

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar aƙalla mutum 18 ƴan bindiga suka sace tare da kashe mutum guda a Angwar Zalla Udawa a Ƙaramar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna. Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani jagora a wurin da lamarin ya faru inda ya ce cikin waɗanda aka sace har da matan aure da ƴan mata. An bayyana cewa ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin 12:30 na daren Asabar wayewar garin Lahadi a garin da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari. BBC ta tuntuɓi mai…

Cigaba Da Karantawa

Dalilin Ficewata A Shirin Labarina – Nafisa Abdullahi

Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta ce daga yanzu ba za ta ci gaba da fitowa a shirin nan mai dogon zango mai suna ‘Labarina’ ba. A sakon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare, tauraruwar ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kanta. Amma wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ta dauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu…

Cigaba Da Karantawa

Duk Matar Da Mijinta Ya Sadu Da Ita Da Karfi Ta Kaishi Kotu – Kwararren Lauya

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wani lauya kuma tsohon sakataren labaran kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Benin, Douglas Ogbankwa, ya bayyana cewa duk mutumin da ya taba matarsa ba yadda ya kamata ba na iya fuskantar laifin lalata da matarsa ma’ana ya aikata fyade. Ogbankwa ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a ranar Alhamis kan ko yana iya yiwuwa mace ta zargi mijinta da laifin aikata fyade a Najeriya, duba ga al’adarmu. Ya ce kafin a kafa dokar hana…

Cigaba Da Karantawa

Na Rantse Da Allah Buhari Rahama Ne Ga ‘Yan Najeriya – Sabon Minista

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sabon karamin ministan ayyuka da gine-gine, Mu’azu Sambo, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki hanyar da ta dace domin bunkasa ababen more rayuwa a kasar. Sabon Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, sannan ya samu tarba daga sakataren din-din-din, Babangida Hussaini, da ma’aikatan ma’aikatar. Sambo ya tabbatar da cewa ’yan Najeriya, wadanda ke shakka a kan iyawar Buhari za su gane muhimmancinsa ne bayan gwamnatinsa ta kare, a…

Cigaba Da Karantawa

Farashin Mai: Sai Mun Kassara Najeriya Da Yajin Aiki – Ƙungiyar Ƙwadago

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar Kwadago NLC, ta dage cewa ma’aikata da talakawa ba za su sake amincewa da karin farashin man fetur da gwamnatin kasar ke shirin yi ba. A sakonsa na barka da arziƙin shigowa sabuwar shekara, shugaban kungiyar ta NLC Ayuba Wabba ya ce har yanzu gwamnati ba ta ja da baya a kan aniyar ta ta ba. ‘’To, kungiyar kwadago ta bayyana matsayinta a kan wannan batu. Mun shaida wa gwamnati a fili cewa ƴan Najeriya sun sha wahala sosai kuma ba…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Yi Tankade Da Rairaya A Kasafin Kudin Shekarar Bana

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da wasu karin ayyuka 6,576 da Majalisar Dokokin ƙasar ta ƙara a kasafin kudin 2022. Shugaban ya ce sanya ayyukan da kuɗinsu ya haura Naira biliyan 36 ya saɓa wa dokar cin gashin kai da kowanne ɓangaren zartarwa ke da shi. Shugaban wanda ya bayyana hakan yayin sanya wa kasafin hannu a fadarsa da ke Abuja, ya ce zai sake mayar wa ƴan majalisar don su duba gyare-gyaren da ya yi. Sai dai shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya kafe a kan cewa babu…

Cigaba Da Karantawa

Ba Za Mu Rungume Hannu Muna Kallon Ana Kisan ‘Yan Najeriya A 2022 Ba – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta rungume hannu tana kallon ƴan bindiga suna ci gaba da kisan jama’a a sabuwar shekarar da aka shiga ba. Shugaban ya ce da yawan ƴan bindigar na miƙa wuya ga dakaru a halin da ake ciki, kuma an samar da tsare-tsare da za su ba su damar ci gaba da yin hakan a wurare daban-daban’. A sakonsa na barka da arziƙin shiga sabuwar shekara, shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ba da…

Cigaba Da Karantawa