Da Dumi-Dumi: Korona Ta Kama Ministan Abuja

Labarin dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Abuja Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar korona. Mai magana da yawun ministan, Abubakar Sani ne ya tabbatar wa BBC da hakan. A wani saƙo da ministan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa bayan ya ji alamun rashin lafiya, ya yanke shawarar yin gwaji wanda bayan gwajin aka tabbatar da ya kamu da cutar. Ministan ya ce a halin yanzu lafiyarsa ƙalau amma yana jin ƙaiƙayi a maƙogwaronsa da kuma jin zazzaɓi da…

Cigaba Da Karantawa

Tukuicin Ƙarshen Shekara Na Mabiya Muryar Ƴanci

Duk wanda ya ƙarasa mana wadannan karin maganganu na Hausa zai samu Nera Dubu Biyar (₦5000) kyauta 💵 😀😊😂 1. A bikin cin nama… 2. Abokin kuka… 3. Dabara ba ya ɗaure kaya… 4. Ganin Hadari… 5. Ko Kura ta karye… A je shafin mu na facebook/muryaryanci.com a amsa su. Sannan kuma a yi “Like 👍🏾” na page ɗin. Muna nan muna sauraren ku. Mun gode. 🙏🏾

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Sanya Hannu A Kasafin Kudin Shekarar 2023

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2022 inda ya zama doka. Kasafin ya kai naira tiriliyan 17.127 wanda aka yi wa laƙabi da kasafin habaƙa tattalin arziƙi da tafiyar da shi. Cikin waɗanda suka halarci sa hannu a kasafin kuɗin har da Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan da Kakakin Majalsar Wakilai Femi Gbajabiamila da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Ministar Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare Zainab Ahmed. Shekarar 2021 mai ƙarewa an yi mata…

Cigaba Da Karantawa

Korona Za Ta Zama Tarihi A Shekarar 2022 – Hukumar Lafiya

Hukumar Lafiya Ta Duniya ta bayyana cewa tana da yaƙinin cewa za a magance annobar korona a shekarar 2022 matuƙar ƙasashe suka haɗa kansu suka yi aiki kafaɗa da kafaɗa. Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan inda ya ce a halin yanzu akwai abubuwan da ake amfani da su domin kare kai da kuma maganin korona amma a cewarsa, iƙirarin kishin ƙasa da kuma ɓoye rigakafi da wasu ƙasashe ke yi ne ya haddasa ɓullar sabon nau’in Omicron na korona. Mista Tedros ya…

Cigaba Da Karantawa

Ina Alfahari Da Masoyana – Jaruma Hafsat Hassan

Wata Sabuwar jaruma a Masana’antar Kannywwod Hafsat Hassan ta nuna yadda take jin dadin ta a game da irin kaunar da mutune su ke nuna Mata tun daga lokacin da suka fara ganin ta a cikin shirin fim. Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya da muka tambaye ta irin yadda ta ke gudanar da rayuwar ta a matsayin ta na Sabuwar jaruma sai ta ke cewa. “To a gaskiya duk da ban dade da fara shirin fim ba, Ina alfahari da ita saboda alamun nasara da…

Cigaba Da Karantawa

Jigawa: An Cigaba Da Saurarar Shari’ar Tsohon Gwamna Saminu Turaki

Rahotannin dake shigo mana daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewar an cigaba da shari’ar tsohon gwamnan jihar Sanata Ibrahim Saminu Turaki a babbar kotun tarayya da ke Dutse babban birnin jihar Jigawa, bayan shekaru goma sha hudu. An ruwaito Saminu Turaki ya bayyana a gaban kotun a ranar 7 ga watan Disamba inda ya ke fuskantar zargi 32 kan wawurar wasu kudi da suka kai N36 biliyan a Baitul Malin Gwamantin Jihar. A shekarar 2007, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa…

Cigaba Da Karantawa

Zan Nemi Kujerar Gwamnan Kaduna A 2023 – Isa Ashiru Kudan

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2019, Hon Isa Kudan Ashiru ya ce shi ya samu nasara a zaben 2019 amma magudi aka tafka masa, amma zai kara tsayawa takarar a shekarar 2023. Ɗan siyasar ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a Kaduna, ya kara da cewa yana siyasa ne don yi wa mutane aiki sannan ya shayar da jama’arsa romon dimokradiyya. Kudan ya ce babu shakka zai kara tsayawa…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: An Yi Nasarar Hallaka ‘Yan Bindiga 38

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar an kashe akalla ‘yan bindiga 38 yayin da ‘yan sanda biyar suka mutu a samame daban-daban da aka kai cikin jihar Katsina. Rundunar ‘yan sanda jihar Katsina ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana karkashin shugaban ‘yan sandan jihar Sanusi Buba. “Babu shakka wannan shekarar da ta kare an fuskanci kalubale mai yawa a Katsina musamman na tsaro, sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta samu nasarori masu yawa a yakin da take da ‘yan bindiga da masu…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Cika Dukkanin Alkawuran Da Ya Yi Wa ‘Yan Najeriya – Fadar Shugaban Kasa

A wani taron manema labarai da ya gudanar, ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce gwamnatin Buhari ta samu nasara a fannoni da dama duk da an fuskanci ƙalubale na tsaro da ta tattalin arziki a shekarar 2021. “A shekara mai ƙarewa, babban ƙalubale shi ne na tsaro. Amma duk da wannan da kuma ƙalubalen tattalin arziki da aka saba samu, wannan gwamnatin ta samu ci gaba sosai kamar yadda za mu bayyana,” in ji Lai Mohammed. Ɓangaren tsaro ya kasance wanda aka fi fuskantar ƙalubale cikin wannan gwamnati…

Cigaba Da Karantawa